Yanzu-Yanzu: Katin zabe ba su lalace ba, INEC ta yi wa Tinubu martani
- Hukumar zabe mai zaman kanta, na Najeriya, INEC, ta yi wa Sanata Ahmed Bola Tinubu martani kan cewa katin zabe sun dena aiki
- Jagoran na Jam'iyyar APC na kasa, Bola Tinubu, ya bayyana cewa an samu ragowar masu zabe ne saboda katin zabe na mutane suna lalacewa
- Sai dai INEC ta musunta hakan, tana mai cewa katin ta ba su dena aiki ba, ta kuma shawarci duk wanda ya yi rajitsa kada ya sake yi
Hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, ta ce katin masu zabe, PVC, ba su lalace ba, Daily Trust ta ruwaito.
Hukumar ta bayyana hakan ne yayin da ta ke mayar da martani kan kalaman da Sanata Bola Tinubu, Jagoran Jam'iyyar APC na kasa ya yi.
Yayin da ya ke karban bakuncin wasu magoya bayansa, Tinubu ya yi ikirarin cewa masu zabe suna raguwa a baya-bayan nan saboda wasu katin zaben sun dena aiki.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Amma, da ya ke martani, Mashawarcin Shugaban INEC, Farfesa Bolade Eyinla, ya ce wadanda suka yi rajista a baya babu bukatar su sake yi domin katin bai gama aiki ba.
Eyinla ya gargadi wadanda suka yi rajista cewa kada su sake yi domin katin da aka basu na PVC a baya-bayan nan lafiyarsu kalau kuma za su iya zabe da su, rahton Daily Trust.
Ya ce:
"Abin da ya fada ba gaskiya bane. Dukkan katin zaben da aka bawa masu zabe a baya-bayan nan za su yi aiki. Irin wannan bayanin ne zai saka mutane su rika zuwa yin rajitsa sau biyu ana samun matsala".
A bangarensa, Babban sakataren watsa labarai na INEC, Mr Rotimi Lawrence Oyekanmi ya ce, yan Najeriya da suka yi rajista ba sai sun sake yi ba.
Ya yi gargadin cewa:
"Yin rajista sau biyu ma laifi ne a dokar mu. Duk wanda shekarunsu ya isa rajista sau daya za su yi. Da sunan mutum ya shiga rajista ta kasa, ba zai sake fita ba."
Oyekanmi ya ce:
"Daya daga cikin yanayin da za a iya cire sunan mutum daga rajistan mu shine idan an nuna kwakwarar hujja da ke nuna mutumin da ke da sunan ya mutu."
Kungiyar Kirista Ta Najeriya Ta Buƙaci Buhari Ya Janye Tallafin Man Fetur Kafin 2023
A wani labarin, kun ji cewa Kungiyar Kirista ta Najeriya, NCF, gammayar mabiya Katolika da Protestant ta ce ya zama dole gwamnatin tarayyar Najeriya ta jajirce ta ceto kasar daga rushewa ta hanyar cire tallafin man fetur, .
NCF ta ce akwai alamu kwarara da ke nuna cewa idan an cire tallafin man fetur, da aka ce yana lashe kimanin Naira biliyan 250 duk wata, tattalin arzikin zai shiga mummunan hali, Guardian ta ruwaito.
A wani taron manema labarai a Abuja, shugaban NCF, Bishop John Matthew, tare da sauran shugabannin kungiyar, sun ce tallafin man fetur babban kallubale ne da ya kamata a tunkare shi gadan-gadan.
Asali: Legit.ng