Shugaba Buhari ya dira birnin Banjul, kasar Gambia don halartan bikin ranstar da Adama Barrow

Shugaba Buhari ya dira birnin Banjul, kasar Gambia don halartan bikin ranstar da Adama Barrow

  • Shugaban kasan Najeriya ya isa kasar Gambia bayan yan sa'o'i da tashi daga Abuja
  • Buhari ya tafi Gambia bisa gayyatar shugaban kasa Adama Barrow bayan lashe zabe karo na biyu
  • Najeriya na cikin kasashen da suka taimakawa Gambia wajen tilastawa tsohon shugaba Yahaya Jammeh sauka daga mulki

Banjul - Shugaba Muhammadu Buhari ya dira Banjul, babbar tarayyar kasar Gambia don halartan bikin rantsar da shugaban kasa Adama Barrow bayan lashe zabe karo na biyu.

Hadimin shugaban kasa na gidajen talabijin da rediyo, Buhari Sallau, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki kuma Legit ta samu.

Yace:

"Shugaba Muhammadu Buhari ya dira Gambia don halartan bikin rantsar da shugaba Adama Barrow."
"Ya samu tarba daga wajen mataimakiyar shugaban kasa, Dr Isatou Touray, da jakadan Najeriya a Gambia, Muhammed Manu Kola a babbar tashar jirgin Banjul."

Kara karanta wannan

2023: Orji Kalu ya gana da Buhari a fadar shugaban kasa, ya ce ya ji dadi sosai

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Adama Barrow
Shugaba Buhari ya dira birnin Banjul, kasar Gambia don halartan bikin ranstar da Adama Barrow Hoto: Sunday Ahgaeze
Asali: Twitter

Buhari zai lula Gambia domin halartan bikin rantsar da Shugaba Adama Barrow

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai je kasar Gambia domin halartan bikin rantsar da shugaban kasarsu, Adama Barrow, wanda zai dare kujerar a karo na biyu a ranar Laraba, 19 ga watan Janairu.

A cikin wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar, ta ce an gayyaci shugaban kasar domin ya zama babban bako a bikin wanda zai samu halartan manyan shugabannin Afrika.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng