Innalillahi: Yan bindiga sun bindige Basaraken Arewa har lahira a cikin gidansa
- Miyagun yan bindiga sun harbe wani Basarake har lahira a cikin gidansa dake karamar hukumar Madagali, jihar Adamawa
- Maharan sun kuma kashe wani yaro ɗan shekara 16, wanda suka yi garkuwa da shi tare da mahaifiyarsa da ɗan uwansa
- Hukumar yan sanda a jihar Adamawa, tace ta tura tawagar jami'an yan sanda yankin domin kamo masu hannu a lamarin
Adamawa - Mahukunta sun tabbatar da kashe mutum biyu a hare-haren garkuwa da mutane na baya-bayan nan a ƙaramar hukumar Madagali, jihar Adamawa.
Yankin Madagali, wanda ya kasance ƙarƙashin ikon kungiyar Boko Haram daga 2014 zuwa 2015, an samu zaman lafiya a yanzun.
Wani mazaunin yankin, ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa, wani matashi Ijarshu Markus, da aka yi garkuwa da shi tare da mahaifiyarsa da ɗan uwansa, ya mutu a hannun yan ta'adda.
Yan Bijilanti dake yankin, sun ceto mahaifiyarsa da kuma ɗan uwan nasa, amma yan bindigan suka yi awon gaba da yaron.
Bayan kwana uku da faruwar haka, mutane suka tsinci gawar yaron ɗan shekara 16 a cikin jeji, ɗauke da raunin wuka a ƙirjinsa da kuma zuciyarsa.
Wane Basarake yan bindiga suka kashe?
Wannan ya zo ne kwanaki bayan wasu yan bindiga sun bindige Magajin Gari, Ahmadu Sikari, da tsakar dare a cikin gidansa.
Yan ta'addan sun yi yunkurin yin awon gaba da Basaraken amma abun ya ci tura, shi ne suka harbe shi har lahira.
Hakimin Duhu, Mustapha Sanusi, yace mutuwar Magajin Gari da kuma Ijarshu ya tada hankulan mutanen yankin, ya yi kira ga gwamnati ta ƙara tsaro a yankin.
Yace:
"Muna kira ga gwamnati ta taimaka mana, ta ƙara yawan jami'an tsaro a yankin, domin yan ta'addan nan ƙara ƙarfi suke."
Hakimin ya nuna cewa yan Boko Haram na haɗa kai da sauran yan ta'adda suna tara kudi ta hanyar garkuwa da neman kudin fansa.
Wane matakin yan sanda suka ɗauka?
Kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Adamawa, DSP Sulaiman Nguroje, ya tabbatar da kashe basaraken da kuma matashin.
Ya kuma ƙara da cewa tuni hukumar yan sandan jihar ta tura tawagar jami'anta domin kamo waɗan da suka yi wannan aika-aika.
A wani labarin na daban kuma Yan bindiga sun kai mummunan hari hedkwatar APC, sun halaka jiga-jigan jam'iyya
Rahoton da muka samu da safiyar nan yace wasu miyagun yan bindiga sun kai mummunan hari ofishin jam'iyyar APC ana tsaka da taron sulhu a jihar Enugu.
Maharan sun bindige jiga-jigan jam'iyyar guda biyu har lahira, sun sace mutum daya, wasu da dama suna matsanancin hali a Asibiti.
Asali: Legit.ng