Da duminsa: Shugaba Buhari ya kaddamar da Dalar Shinkafa milyan daya a Abuja
- Watanni biyu bayan barazanar damke manoman shinkafa da suka ki biyan bashi, CBN ta fitar da sabon tsarin dalar tara Shinkafa
- Shugaban kasa ya kaddamar da buhuhunan shinkafa milyan daya da aka noma a nan gida Najeriya
- Shirin Anchor Borrowers Programme (ABP) na daya daga cikin tallafin da Gwamnati ta fito da su a 2015
- Gwamnatin tarayya ta hannun bankin CBN ta bada bashin miliyoyin kudi ga manoma don inganta harkokinsu
FCT Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da Dalar Shinkafa milyan daya da kungiyar manoman shinkafa RIFAN ta tara a birnin tarayya Abuja.
Buhari ya kaddamar da wannan dala ne a ranar Talata, 18 ga watan Junairu, 2022, a farfajiyar cibiyar kasuwanci da masana'atun Abuja ACCI dake unguwar Lubge Abuja.
An tara wadannan buhuhunan shinkafa milyan daya ne a dala-dala goma sha biyar (15).
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Babbar bankin Najeriya (CBN) da kungiyar manoman shinkafa Najeriya (RIFAN) ne suka hada kai wajen wannan shiri.
Wadanda ke hallare a taron sun hada da Gwamna Kayode Fayemi na jihar Ekiti, Gwamna Atiku Bagudu na jihar Kebbi, Gwamna Ben Ayade na Cross Rivers, Gwamna David Umahi na Ebonyi da Abubakar Badaru na Jigawa.
Karkashin shirin Anchor Borrowers’ Program, an tattaro buhuhunan shinkafa milyan daya daga jihohin Najeriya don gina dalar.
An bukaci manoma su kawo buhuhunan shinkafan ne gwamnati ta saya ta basu kudi don su biya bashin da suka karba.
Zamu damke manoman da suka ki biyan bashin da muka basu, CBN
A bayan mun kawo muku cewa CBN ya fara barazanar amfani da yan sanda wajen damke manoman da suka ki biyan bashin da suka karba karkashin shirin Anchor Borrowers Programme(ABP).
A 2015, Gwamnati ta baiwa manoman shinkafa da wasu tsirrai kudade don inganta aikin noma a Najeriya.
CBN yace ba zai cigaba da lamuntan abinda manoman ke yi na ganin kyauta aka basu kuma kuma duk wanda bai biya ba zai shiga komar hukuma.
Idris ya bayyana cewa yawancin wadanda suka ki biyan bashin manoman Shinkafa ne, Nairametrics ta ruwaito.
Asali: Legit.ng