Da Dumi-Dumi: Mutane sun mutu, yayin da Sojoji da Yan bindiga suka shafe awanni suna gumurzu a Kaduna
- Sojojin Najeriya sun samu nasarar dakile harin yan bindiga da safiyar nan a jihar Kaduna, bayan shafe awanni suna musayar wuta
- Magajin garin da lamarin ya faru, yace maharan sun shigo da tsakar dare da nufin sace mutane, amma suka kwashi kashin su a hannun sojoji
- Jihar Kaduna na ɗaya daga cikin jihohin arewa ta yamma dake fama da ayyukan ta'addancin yan bindiga a Najeriya
Kaduna - Dakarun sojin Najeriya sun yi gumurzu da wasu yan bindiga a Unguwar Musa Tudun Wada Kudansa dake Maraban Rido, karamar hukumar Chikun, jihar Kaduna.
Daily Trust ta rahoto cewa sojojin sun fafata da yan ta'addan ne da sanyin safiyar yau Talata, 18 ga watan Janairu, 2022.
Kowane bangare tsakanin sojojin da kuma yan bindigan an musu ɓarna, lamarin da ya jefa al'ummar dake yankin cikin tashin hankali.
Meya haddasa musayar wutan?
Basaraken dake yankin, Joseph Sauri Garba, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin ga manema labarai, yace gumurzun ya shafe awanni uku ana fafatawa tsakanin sojojin da yan bindiga.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Rahotanni sun tabbatar da cewa yan bindigan sun farmaki yankin ne da tsakiyar dare da mummunan nufin su na sace mutanen dake rayuwa a wurin.
A baya-bayan nan, gwarazan dakarun sojin Najeriya sun kwato kusan mutum 10 da yan bindiga suka sace a yankin.
Yan sanda sun samu rahoton abinda ya faru?
Da aka tuntubi kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Kaduna, ASP Muhammad Jalige, ta wayar salula, bai ɗaga kiran ba, bare a ji ta bakin hukumar su.
Yan bindiga, waɗan da gwamnatin tarayyan Najeriya ta ayyana su a matsayin yan ta'adda, suna cigaba da ƙaddamar da hare-hare a ƙauyukan jihar Kaduna, dake arewa maso yamma.
A wani labarin na daban kuma Mutane sun shiga daji sun kwato Sarkin su da yan bindiga suka sace a Filato
Mutane sun haɗa kai da taimakon jami'an tsaro, sun shiga cikin jeji neman Sarkin su da yan bindiga suka sace, sun samu nasarar ceto shi.
Sojojin Operation Safe Haven tare da haɗin guiwar sauran hukumomin tsaro da yan Sakai sun kame mutum biyu da ake zargi da sace Sarkin.
Asali: Legit.ng