Da Dumi-Dumi: Mutane sun shiga daji sun kwato Sarkin su da yan bindiga suka sace a Filato
- Mutane sun haɗa kai sun shiga cikin jeji neman Sarkin su da yan bindiga suka sace, sun samu nasarar ceto shi
- Sojojin Operation Safe Haven tare da haɗin guiwar sauran hukumomin tsaro da yan Sakai sun kame mutum biyu da ake zargi
- Jama'ar dake yankin Masarautar Basaraken sun nuna farin cikin su, kuma tuni ya isa ga iyalansa
Plateau - Basaraken masarautar Vwang, Da Gyang Gutt Balak, wanda yan bindiga suka sace ranar Lahadi da ta gabata a NIPPS kuru, jihar Filato, ya kubuta.
The Nation ta rahoto cewa wasu da ake zaton yan bindiga ne sun yi awon gaba da Basaraken a hanyarsa ta komawa gida a Vom ranar Lahadi.
Shugaban ƙungiyar matasan Berom, (BYM), Barista Emmanuel Mandung, shine ya tabbatar da kubutar sarkin ga manema labarai.
A jawabinsa yace:
"Nasara ta Allah ce, muna ƙara godiya ga Allah bisa dawowar sarkin mu cikin koshin lafiya, Mai girman daraja, Basaraken Vwang, Da Gyang Gutt Balak, wanda aka sace jiya."
"Muna tsantsar godiya ga Allah bisa ni'imar da ya mana na kare rayuwar Sarkin mu mai daraja. Mu mutanen masarautar Vwang, muna gode wa al'umma bisa Addu'a da kuma nuna mana soyayya bayan sace Sarki."
"Yanzu haka Sarkin mu ya dawo, kuma cikin koshin lafiya, ina taya mu murna baki ɗaya."
Shin dagaske mutane suka kwato shi?
Rahotanni sun bayyana cewa mutanen yankin ne suka haɗa kai, suka shiga daji nemo sarkin da kuma wajen Duwatsu, wanda hakan ya haifar da ɗa mai ido, suka samu nasarar ceto shi.
Kakakin rundunar sojin Operation Safe Haven, Manjo Ishaku Takwa, ya tabbatar da ceto Basaraken a hukumance.
Punch ta rahoto a sanarwar da ya fitar yace:
"Tun bayan faruwar lamarin, kwamandan Operation Safe Haven, Manjo Janar Ibrahim, ya umarci sojoji su bazama neman Basaraken"
"Sojojin da sauran hukumonin tsaro, mafarauta da yan Bijilanti, suka kaddamar da harin bincike yankunan Duwatsu, da suka haɗa da Sabon Gida Kanal, Gero da Dahol."
"Sun cafke mutum biyu da ake zargi a wani kangon gini, kuma hakan yasa maharan suka sako Basaraken. Tuni ya isa cikin iyalansa."
A wani labarin kuma Bayan ganawa da Buhari, Matawalle ya bayyana mutanen dake rura wutar ta'addanci a Zamfara
Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara, ya bayyana cewa akwai mutanen da ba zu bari a kawo karshen matsalar tsaro ba.
Gwamnan yace suna amfani da rashin tsaro wajen sukar gwamnati a wurin yan kasa, domin su samu nasara a siyasance.
Asali: Legit.ng