Innalillahi: Wani ma'aikacin majalisar dokoki ya yanki jiki ya fadi matacce
- Labarin da ke iso mu ya bayyana cewa, wani ma'aikacin majalisar dokokin kasar nan ya yanki jiki ya fadi matacce
- Rahoton ya bayyana yadda lamarin ya faru, inda yace abokan aikinsa sun yi kokarin kai masa agajin gaggawa amma rai ya yi halinsa
- Abdul Olajide Abayomi mai shekaru 34 ya rasu ne a yau Litinin jim kadan bayan fadowarsa a matakalan majalisar
Abuja - A ranar Litinin ne wani ma’aikacin majalisar dokokin kasar nan ya yanki jiki ya fadi ya mutu yayin da ya tattaka hawa na biyu na fadar White House, The Nation ta ruwaito.
Shedun gani da ido sun ce Abdul Olajide Abayomi, mai shekaru 34, ya yanki jiki ya fadi a saman matakalan saman benen.
Nan take ya mirgina zuwa matakalar saukowa kafin a zo a taimaka masa.
Masu aikin tsaftace muhalli, wadanda suka gan shi lokacin da ya fado, an ce sun sanar da ma’aikata inda suka kai masa agaji nan take.
An ce abokan aikinsa sun garzaya da shi asibitin majalisar dokokin domin duba lafiyarsa amma ya mutu a kan hanyar zuwa asibitin.
An ce ya mutu ne sakamakon bugun zuciya da wasu cututtukan da ke da alaka da hakan.
Ya kasance yana aiki tare da Sashen Inter-Parliamentary a karkashin Daraktan Inter-Parliamentary and Protocols na majalisar dokokin kasa.
Har ila yau, an ce wani ma’aikacin wucin gadi ya fado daga sama a lokacin da yake aiki a hawa na hudu na rukunin majalisar dokokin kasar wanda hakan ya kai shi ga jin raunuka.
Shugaban EFCC ya yanki jiki ya fadi yayin da yake magana a dakin taro
Shugaban Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC), Abdulrasheed Bawa ya yanki jiki ya fadi a bikin ranar kasa ta uku a Banquet Hall Villa, Tribune Nigeria ta ruwaito.
Bawa wanda ke isar da sakon fatan alheri ba zato ba tsammani ya carke, ya koma kan kujerarsa, ya yanki jiki ya zube.
Bawa ya tsaya da magana ya rufe fuskarsa da tafin hannunsa na dama, yana mai cewa:
"Don Allah, ku gafarce ni, ba zan iya ci gaba ba."
Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Dijital, Farfesa Isa Pantami, da wasu manyan mutane sun rike shi, bayan wani lokaci, aka yi masa jagora ya fita daga zauren taron.
A cewar rahoton Daily Trust Jagoran Bikin (MC) daga baya ya ba da sanarwar cewa yanayin Bawa ya dan warware.
A wani labarin, Sulaiman Uba Gaya, wani babban ‘dan jarida a Najeriya, ya bada labarin alherin da Alhaji Bashir Othman Tofa ya yi masa shekaru talatin da suka wuce.
A wani rubutun ta’aziyya da ya yi a Sun, Sulaiman Uba Gaya ya tuno yadda tsohuwar kyautar da Bashir Othman Tofa ya taba yi masa da ta taimake shi.
Wannan mutumi ya hadu da Alhaji Tofa ne a lokacin ya na gwauro, ya fara aikin jarida a jihar Kano.
Asali: Legit.ng