Ina mata fatan alkhairi, amma mafi alkhairin mutum muke bukata a 2023: Gwamnan Oyo ga Tinubu

Ina mata fatan alkhairi, amma mafi alkhairin mutum muke bukata a 2023: Gwamnan Oyo ga Tinubu

Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, a ranar Asabar ya bayyanawa jagoran jam'iyyar All Progressives Congress APC, Bola Tinubu, cewa mafi alkhairi Najeriya ke bukata yanzu.

Makinde ya bayyana hakan ne yayinda ya karbi bakuncin Tinubu a ziyarar ta'azziyar mutuwar manyan yan jihar Oyo uku da suka mutu kwanakin nan.

Mamban kungiyar maso goyon bayan Tinubu, Jubril Aremu Gawat, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Asabar.

Cikin makonni biyu, jihar Oyo ta yi rashin Sarkin Ibadan, Oba Saliu Adetunji; Sarkin Ogbomoso, Oba Jimoh Oyewumi Ajagungbade da tsohon Gwamnan jihar, Christopher Alao-Akala.

Makinde yace:

"Mun gode maka bisa ziyarar da ka kawo kuma mun gode ka ajiye siyasa a gefe ka kawo mana ziyara lokacin da muke jimami."

Kara karanta wannan

Dalilin da yasa na ki aure tun bayan mutuwar Maryam Babangida, IBB

"Ina son amfani da wannan dama wajen yi maka fatan alkhairi bisa neman shugabancin kasar nan da kake yi. Mafi Alkhairi muke so ga kasar nan yanzu."

Ina mata fatan alkhairi, amma mafi alkhairin mutum muke bukata a 2023: Gwamnan Oyo ga Tinubu
Ina mata fatan alkhairi, amma mafi alkhairin mutum muke bukata a 2023: Gwamnan Oyo ga Tinubu Hoto: Jubril Aremu Gawat
Asali: Facebook

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel