Kasafin kudin 2022: Gwamnan Plateau zai kashe N100m wajen gyara gidan sauke bakinsa
- Kwamishanan kasafin kudin jihar Plateau ya yi fashin baki kan kudaden da gwamnatin jihar ke shirin kashewa a 2022
- Kudin da aka ware don gyaran gidan saukan bakin gwamnan ya janyo cece-kuce a kafafen sada zumunta
- Gwamna Simon Lalong ya rattafa hannunsa kan kasafin kudin 2022 tun watar Disamba 2021
Gwamnatin jihar Plateau za ta kashe kudi N100,000,000.00 don gyara gidan saukan bakin Simon Lalong yayinda gaba daya ma'aikatar al'adu da bude ido zata kashe N88,000,000.00.
Hakazalika an samu tanakudi cikin kudin da aka shirya gina titin saman British American da ke shataletalen Lamingo.
Kwamishanan kasafin kudi da shirye-shirye tattalin arzikin jihar, Sylvester Wallangko, ya bayyana haka yayin fashin baki kan kasafin kudi 2022 ranar Juma'a, rahoton Vanguard.
Wallangko ya bayyana cewa kasafin kudin 2022 ba kai yawan na 2021 ba saboda an samu ragin N40bn daga N147bn a 2021 zuwa N106bn a 2022.
A cewarsa:
"An warewa Ma'aikatar al'adu, da bude ido N88,000,000.00....za'a gina sashen manya a tashar jirgin saman kasa da kasa, Heipang a kudi N60,000,000.00, za'a gyara gidan saukar bakin Simon Lalong da kudi N100,000,000.00."
Bayan rikici ya lafa a Filato, an sake hallaka Bayin Allah a wani danyen harin tsakar dare
A wani labarin kuwa, kungiyar Irigwe Development Association ta koka kan kisan mutanenta da ta ce an yi a kauyen Ancha, yankin Miango a karamar hukumar Bassa.
Rahoton da muka samu a ranar Laraba, 12 ga watan Junairu, 2021 shi ne an kashe mutum 18 a Ancha a wani hari da ‘yan bindiga suka kai a kasar Rigwe.
Mai magana da yawun bakin kungiyar Irigwe Development Association, Mr. Davidson Malison ya aikawa jaridar Vanguard jawabin da suka fitar bayan harin.
A jawabin na Davidson Malison, ya ce da kimanin karfe 12:00 na daren ranar Talata ne ‘yan bindiga suka duro kauyen Ancha, suka yi mummunan ta’adi.
Asali: Legit.ng