Labarin cikin Hotuna: Shugaba Buhari ya halarci faretin tunawa da Sojojin da suka mutu faggen fama
Shugaba Muhammadu Buhari tare da manyan jiga-jigan Gwamnatin Najeriya sun halarci taron bikin ranar tunawa da dakarun Sojin Najeriya da suka hallaka a faggen fama.
A kowace ranar 15 ga Junairun shekara, ana bikin tunawa da Sojojin Najeriya da aka rasa yayin kare mutuncin Najeriya.
Yayinda sauran kasashen duniya ke bikin ranar 11 ga Nuwamba, ana yi 15 ga Junairu a Najeriya saboda ranar aka kawo karshen yakin basasa a 1970.
A taron da aka yi a farfajiyar Eagle Square dake birnin tarayya Abuja, Shugaba Buhar ya jagoranci sanya firen girma don karrama Sojojin.
Daga bisani kuma ya kalli faretin Sojojin.
Wadanda suka halarci taron sun hada da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo; Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan; Kaakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila; da Alkalin Alkalai, Tanko Muhammad.
Hakazalika akwai Shugaban hafsan tsaron Najeriya CDS, Janar Lucky Irabor; Shugaban hafsan Sojin Kasa, Laftanan Janar Farouq Yahaya; Shugaban hafsan Sojin sama, Isiaka Amao, da Shugaban Sojin ruwa, Admiral Awwal Zubairu Gambo.
Asali: Legit.ng