Da Ɗumi-Ɗumi: An bindige sufetan 'yan sanda har lahira a cikin caji ofis
- Wasu bata gari da ake zargin 'yan bindiga ne sun kai hari hedkwatan ofishin 'yan sanda da ke Mgbidi a Jihar Imo
- Sun isa wurin ne cikin wata mota kirar Toyota Hilux fara suka fara harbe-harbe da nufin kutsawa cikin ofishin yan sandan
- Amma jaruman yan sandan da ke ciki sun dakile harin sun fatattake su sai dai dan sanda daya mai mukamin sufeta ya rasu yayin artabun
Jihar Imo - An bindige wani dan sanda mai mukamin sufeta a caji ofis da ke Mgbidi a hedkwatar rundunar da ke Jihar Imo.
Daily Trust ta ruwaito cewa an kashe dan sandan ne a lokacin da yan bindiga suka kai hari a daren ranar Juma'a.
Dubu ta cika: Wani mutum ya shiga hannu yayin da ya kashe yaransa uku ya adana gawarwakinsu a cikin firinji
Kakakin 'yan sanda ya tabbatar da harin
Mai magana da yawun yan sandan jihar, Micheal Abattam, ya tabbatar da harin amma ya ce an fatattaki yan bindigan.
Ya ce:
"A ranar 14 ga watan Janairun 2022 misalin karfe 8.45 na dare, Tawagar yan sanda a caji ofis na Mgbidi sun dakile harin da wasu yan daba cikin wata farar Hilux suka kawo suna harbe-harbe, sun yi yunkurin shiga caji ofis din amma jaruman yan sanda suka dakile harin.
"Sun yi musayar wuta da yan daban. Yayin hakan, an ci galaba kan maharan, wasu daga cikinsu sun jikkata, sun juwa sun tsere a cikin motarsa Toyota Hilux. Kuma yan sandan sun raka su da ruwan wuta.
"Bayan haka, an fara bincike da nufin kamo yan daban duba da cewa ba za su iya nisa ba saboda irin illar da aka yi musu.
"Sai dai yayin arangamar, wani sufetan yan sanda ya rasu, yayin da wani jami'in ya samu kankanin rauni a hannunsa."
Ya kara da cewa kwamishinan yan sandan jihar, CP Rabiu Hussaini, ya yaba wa jami'an bisa jarumtakarsu ya kuma bukaci kada su yi kasa a gwiwa har sai an ga karshen dukkan bata gari.
Ya kuma yi kira ga mutanen Jihar Imo su cigaba da bada hadin kai ga hukumomin tsaro musamman yan sanda ta hanyar basu bayanan sirri a kan lokaci, su kuma bada rahoton duk wanda suka gani da raunin bindiga.
Sojoji sun gasa wa 'yan ISWAP ayya a hannu yayin da suka kai hari a Biu
A wani labarin, mayakan kungiyar ta'addanci ta Islamic State West Africa Province, ISWAP, a ranar Asabar, sun kai hari Mainahari a kusa da Wakabu a karamar hukumar Biu ta Jihar Borno, The Punch ta ruwaito.
A cewar wata majiya daga barikin sojoji a Biu, 'yan ta'addan sun harba bama-bamai a kauyen misalin karfe 3 na rana.
Sai dai, dakarun sojojin Najeriya sun yi nasarar fatattakar 'yan ta'addan.
Asali: Legit.ng