Kungiyar Zamfara Circle ta taimakawa yan gudun hijra da kayan abinci

Kungiyar Zamfara Circle ta taimakawa yan gudun hijra da kayan abinci

  • Wata kungiyar matasa sun tara sama da milyan goma don taimakawa yan gudun hijra a jihar Zamfara
  • Bayan kasa da makonni biyu da tara kudin, kungiyar ta fara raba kayan abinci ga iyalai
  • Kungiyar na cigaba da kira ga gwamnatin jihar Zamfara ta mayar da hankali kan iyalan da rikicin yan bindiga ta kora daga muhallansu

Zamfara - Kungiyar Zamfara Circle Initiative ta raba kayan abinci ga wasu jama'an jihar Zamfara da hare-haren yan bindiga ya tilasta musu guduwa daga muhallansu.

Wannan kungiyar da Barista Audu Bulama Bukarti ya jagoranci tara kudi ta fara rabon kayan abinci ga iyaye mata a jihar Zamfara.

A farko shekarar nan, Audu Bukarti, wanda dalibin Doktora ne a jami'ar SOAS dake Birtaniya ya koka kan irin halin da wasu mutane da yan bindiga suka fitittika daga muhallansu suke ciki.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda suna neman wuce gona da iri a jihohin mu, Zulum da Matawalle sun koka

Ya yi kira ga gwamnatin jihar Zamfara ta tattara wadannan mutane a waje guda, kamar sansanin yan gudun Hijra.

Daga bisani suka fara tara kudi don sayen kayayyaki.

A bayanin karshe da yayi kan yunkurin tara kudin, ya bayyana cewa an samu sama da milyan 10.

Kungiyar Zamfara Circle ta taimakawa yan gudun hijra da kayan abinci
Kungiyar Zamfara Circle ta taimakawa yan gudun hijra da kayan abinci
Asali: Facebook

Bayan mako guda da sanarwa, Audu Bulama ya bayyana bidiyo da hotunan yadda aka fara rabon kayayyakin da aka saye da kudin.

A bidiyon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, yace:

"Alhamdulillah. Taimakon da kuka tara wa ‘yan’uwanmu na Zamfara ya fara shiga hannunsu. Za mu kawo ci gaba da kawo cikakkun bayanan insha’Allah. Allah Ya saka ma kowa da mafificin alheri."

Kalli bidiyon:

Yayinda Legit Hausa ta tuntube Audu Bulama Bukarti, ya bayyana mana yadda aka tattara wadannan makudan kudade don taimakawa yan gudun Hijran.

Kara karanta wannan

Jihar Neja: Shugaban karamar hukuma ya fadi yadda 'yan bindiga suka kashe mutane a masallaci

A cewarsa, wannan alama ce dake nuna matasan Arewacin Najeriya suna da niyyar taimakon marasa hali da wadanda ke cikin halin kunci.

A cewarsa:

"Babban abin farin ciki da wannan yunkurin shine yadda bayin Allah, mafi yawa matasa, suka nuna jin kai da kishin‘yan’uwansu suka taimaka."
An tara wandannan miliyoyin ne da taro da sisi. Kaga wannan ya ke nuna cewa samarinmu sun farka, kuma wata sabuwar Najeriya inda taimakekeniya zai zama kanbunmu na daf da haifuwa."

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng