'Ya'yan tsohon shugaban sojojin Najeriya sun maka kawunsu a gaban kotu kan dukiyar mahaifinsu
- Lauyan 'ya'yan marigayi shugaban rundunar sojin ƙasa a Najeriya, Janar Luka. N Yusuf, sun gurfanar da kawunsu a gaban kotu a Kaduna
- A takardar shigar da kara mai ɗauke da sakin layi 15, masu shigar da kara sun roki kotu ta taimaka wajen dawo musu da dukiyar mahaifin su
- Kawun su, Emmanuel Yusuf, ya handame musu kadarar dake Anguwar Narayi a cikin Kaduna, a cewarsu
Kaduna - 'Ya'yan marigayi hafsan sojojin ƙasa a Najeriya, Janar Luka. N Yusuf, sun gurfanar da kawunsu, Emmanuel Yusuf, a gaban kotun majistire dake zamanta a Kaduna.
Leadership ta rahoto cewa ƴaƴan marigayin sun bukaci kotu ta kwato musu hakkin su na wata kadara da kawun su ke neman kwace wa.
A karar mai lamba KDC/734cc/21 da Bilhatu Beauty Yusuf, ya shigar a madadin yan uwansa, ya roki kotu ta taimaka musu wajen dawo musu da hakkin su.
Nasrun Minallah: Sojojin NAF sun ceto yan kasuwan da yan bindiga suka sace a hanyar Birnin Gwari-Kaduna
A cewarsa, kadarar na nan a No. 15, kan hanyar Bourmediene, Anguwar Narayi High Cost, cikin garin Kaduna, kuma a halin yanzun kawun su ke amfani da ita.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Lauyan masu shigar da ƙarar, Barista D.B. Kwajaffa, ya bayyana cewa waɗan da yake kare wa suke da haƙƙin mallakar kadarar gidan mahaifinsu dake Narayi a Kaduna.
Amma wanda ake ƙara ya mallake gidan da sunan yana da lasisin mallaka, wanda tuni aka soke lasisin tun a ranar 25 ga watan Oktoba. 2021, inji Lauyan.
Ta ya dukiyar taje hannun kawunsu?
Karar mai ɗauke da sakin layi 15, ta yi bayani dalla-dalla a sakin layi na 9 cewa, wanda ake ƙara ya samu izinin zama a wannan wuri da ake cece kuce daga marigayya mahaifiyar masu ƙara, Bilki Mary Yusuf.
Wani sashin takardan karar yace:
"Ƴaƴan marigayi COAS sun baiwa kawun nasu wa'adi ya tashi daga wurin a rubuce, domin dawo da dukiyar su, amma ya ƙi, ya yi watsi da lamarin."
A wani labarin na daban kuma wani Shugaban karamar hukuma a Najeriya ya yanke jiki ya fadi, ya rigamu gidan gaskiya bayan an kai shi a Asibiti
Emmanuel Leweh, ciyaman na ƙaramar hukumar Akwanga, dake jihar Nasarawa, ya rasu ne bayan ya yanke jiki ya faɗi jim kaɗan bayan fitowa daga taro.
Mista Leweh, wanda ya kwashe watanni uku kacal a ofishin ciyaman na Akwanga, ya mutu ne a wani Asibitin kuɗi dake babban birnin tarayya Abuja , ranar Alhamis.
Asali: Legit.ng