Hotunan Buhari yayin da ya ziyarci iyalan Marigayi Shonekan don yi masu ta’aziyya
- Shugaba Muhammadu Buhari ya ziyarci iyalan tsohon shugaban kasa, Ernest Shonekan a gidansa da ke yankin Ikoyi, jihar Lagas
- Buhari ya kai ziyarar ne domin mika ta'aziyyarsa a kan babban rashi da suka yi na jigon kasar
- Ya kuma samu rakiyar gwamnan jihar Lagas da takwarorinsa na Ogun da Yobe
Lagos - Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ziyarci gidan tsohon shugaban kasa, Marigayi Ernest Shonekan, domin yiwa iyalansa ta'aziyyar rashin sa.
Vanguard ta rahoto cewa Buhari ya ziyarci gidan marigayin da ke jihar Lagas ne a yau Alhamis, 13 ga watan Janairu.
Idan za ku tuna Shonekan ya jagoranci al'amuran Najeriya a matsayin shugaban rikon kwarya tsakanin ranar 26 ga watan Agusta zuwa 17 ga watan Nuwamban 1993, bayan Janar Ibrahim Babangida ya sauka a matsayin shugaban mulkin soji.
Buhari wanda ya kai ziyarar aiki na kwana daya jihar Ogun don kaddamar da wasu ayyuka, ya samu rakiyar gwamnan jihar Lagas, Babajide Sanwo-Olu zuwa gidan marigayin da ke yankin Lugard Avenue, Ikoyi.
Daga cikin wadanda suka yi masa rakiya harda gwamnan jihar Ogun, Prince Dapo Abiodun da takwaransa na jihar Yobe, Mai Mala Buni.
Shugaban kasar da mukarrabansa wadanda suka isa gidan Shonekan da misalin karfe 4:40 na yamma sun samu tarba daga ahlin marigayin.
Buhari ya tsaya a Lagas ne a hanyarsa ta zuwa Abuja sannan ya ware dan lokaci domin mika ta'aziyya ga iyalan tsohon shugaban kafin ya koma Abujan.
Ya jajantawa iyalan mamacin bisa rasuwar jigon su, wanda ya rasu a Legas a ranar Talata, 11 ga watan Janairu yana da shekaru 85 a duniya.
A ruwayar Premium Times, ta ce an zuba matakan tsaro sosai na sojoji, yan sanda da jami'an NSCDS a ciki da kewayen gidan yayin ziyarar shugaban kasar.
An tattaro cewa an zuba akalla motocin fatrol 20 na sojoji da yan sanda a kewayen gidan da ke Ikoyi.
Shugaba Buhari ya bada umurnin rage tsayin tutar Najeriya sakamakon mutuwar Ernest Shonekan
A baya mun kawo cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya yi alhinin mutuwar tsohon shugaban kasan rikon kwarya, Cif Ernest Shonekan wanda ya mutu ranar Talata, 11 ga Junairu, 2022.
Buhari ya bada umurnin rage tsayin tutar Najeriya a fadin tarayya saboda nuna jimamin mutuwar tsohon shugaban.
Ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook. A cewarsa, za'a yi wannan na tsawon kwanaki uku.
Asali: Legit.ng