Jami'an tsaro sun ceto daliban Plateau Poly da yan bindiga suka sace

Jami'an tsaro sun ceto daliban Plateau Poly da yan bindiga suka sace

  • An sace wasu daliban makaranta a sabon harin da yan bindiga suka kai gidajen daliban a jihar Plateau
  • Rahotanni sun nuna cewa akalla dalibai biyu zuwa uku akayi awon gaba da su ranar Laraba
  • Hukumar yan sandan jihar ta tabbatar da cetonsu kuma an hadasu da iyalansu

Barkin Ladi - Jami'an Sojin rundunar operation safe haven (OPSH) da jami'an yan sanda a jihar Plateau sun ceto daliban kwalejin fasaha uku da yan bindiga suka sace.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, Ubah Ogaba, ya bayyana ceton a jawabin da ya saki ranar Alhamis, rahoton TheCable.

Yace:

"Gamayyar yan sanda da Sojin OPSH sun ceto wadanda aka sace jiya a kauyen Ban kuma da kwalejin fasahar jihar Plateau."
"An cetosu yau misalin karfe 2:30 na rana cikin koshin lafiya kuma suna tare da yan sanda."

Kara karanta wannan

Saboda tsabar gudu, Direban tirela ya kashe yara biyu a gaban shagon mahaifiyarsu

Ogaba yace jami'an na kokarin damke masu garkuwa da mutanen.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jami'an tsaro sun ceto daliban Plateau Poly da yan bindiga suka sace
Jami'an tsaro sun ceto daliban Plateau Poly da yan bindiga suka sace
Asali: Twitter

Kakakin rundunar operation safe haven (OPSH), Ishaku Takwa, yace jami'an da aka tura Nding Sesut a karamar hukumar Barkin Ladi sun tsinci daliban cikin wani gonan kaji.

Yace tuni an mayar da su wajen iyalansu.

Yan bindiga sun kai hari Plateau Poly, sun kwashe dalibai

Mun kawo muku cewa yan bindiga masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da akalla dalibai mata biyu na kwalejin fasahar jihar Plateau a harin da suka kai da yammacin Laraba, 12 ga Junairu, 2022.

TVC ta ruwaito cewa yan bindiga sun dira gidajen kwanan dalibai dake wajen makaranta inda suka fara harbi kan mai uwa da wabi kafin sukayi awon gaba da dalibai biyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel