Tashin Hankali: Yan bindiga sun kai hari babbar Sakateriyar jam'iyyar PDP
- Wasu yan bindiga ɗauke da muggan makamai da ake zargin yan daban siyasa ne sun farmaki sakatariyar PDP reshen jihar Ekiti
- Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun yi raga-raga da kujeru, sun lalata fayil-fayin, sannan kuma suka farfasq gilasan kofofi da tagogi
- Tsohon gwamna Fayose, ya yi Allah wadai da mummunan lamarin, ya kuma gargaɗi duk me hannu ya kuka da kansa
Ekiti - Mutane sun shiga tashin hankali a Ado-Ekiti, babban birnin jihar Ekiti, yayin wasu ƴan bindiga da ake tsammanin yan daban siyasa ne suka farmaki babbar Sakateriyar PDP reshen jihar.
Maharan sun yi kaca-kaca da ginin Sakateriyar PDP dake a yankin Ajiosun, kusa da hanyar Ado-Ikere a babban birnin jihar, Ado-Ekiti, da safiyar yau.
The Nation ta rahoto cewa maharan ɗauke da makamai masu hatsari sun farmaki Sakateriyar ne da misalin ƙarfe 8:55 na safe, inda suka rugurguza kujeru, suka lalata fayil-fayin, kuma suka fasa gilasan kofofin da taga.
Rahotanni sun bayyana cewa ma'aikatan wurin sun tsere domin neman mafaka yayin harin, kuma lamarin ya jefa mutanen yankin cikin tashin hankali.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Shin yan sanda sun samu rahoto?
Da muka tuntubi kakakin hukumar yan sanda reshen jihar Ekiti, ASP Sunday Abutu, ya tabbatar mana da faruwar lamarin.
Ya kuma ƙara da cewa tuni hukumar su ta jibge jami'an yan sanda a yankin domin daƙile duk wata tashin-tashina da ka iya biyo baya.
Kakakain yan sandan ya bayyana cewa sun kame wasu da suke zargin suna da hannu a lamarin, kuma hukumar yan sanda ta fara gudanar da bincike don gano dukkan masu alaƙa da harin.
Fayose ya yi Allah wadai da harin
Tsohon gwamnan jihar, Ayodele Fayose, ya yi Allah wadai da harin, ya kuma yi kira ga hukumomin tsaro su gaggauta kamo masu hannu domin su girbi ɗanyen aikin da suka shuka.
Fayose, a wata sanarwa da ya fitar ɗauke da sa hannun sa, yace wannan bakon abu ne da har wani a jihar Ekiti zai jefa kansa cikin aikata babban laifi kamar wannan.
Tribune ta rahoto Fayose yace:
"An jawo hankali na kan wani hari da yan daba suka kai sakateriyar PDP ta jihar Ekiti. Ya zama wajibi yan sanda su gano su, domin su fuskanci fushin doka."
"Wannan ya zama na ƙarshe da za kaiwa kayan PDP ko mambanta hari a jihar Ekiti, kuma duk masu hannu a irin haka su shiga taitayin su."
A wnai labarin na daban kuma An rangaɗa wa shugaba Muhammadu Buhari sabbin sunaye biyu a jihar Ogun
A yau ne shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya fara ziyarar aiki ta kwana ɗaya a jihar Ogun dake kudu maso yammacin ƙasar nan.
Yayin wannan ziyara shugaba Buhari, wanda ya fara aikin soja a Abeokuta, ya samu sabbin sunaye biyu da aka raɗa masa.
Asali: Legit.ng