Gwamna ya yi alakawarin milyan biyar ga duk wanda ya fallasa dan bindiga a jiharsa

Gwamna ya yi alakawarin milyan biyar ga duk wanda ya fallasa dan bindiga a jiharsa

  • Gwamnan jihar Imo, ya sa ladan miliyan N1m da N5m kan duk wani mutum da ya fallasa bayanai aka kama ɗan bindiga ko aka gano maɓoyarsu
  • Hope Uzodinma, yace yan bindiga sun tafka aika-aika, amma gwamnatinsa ta ɗauki matakan kawo ƙarshen su baki ɗaya
  • Jihar Imo na ɗaya daga cikin jihohin kudu maso gabas da matsalar yan bindiga da yan IPOB ta yi wa katutu

Imo - Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo dake kudancin Najeriya, ya sa tsabar kudi miliyan N1m da Miliyan N5m ga duk mutum ko ƙungiyar da ta bada bayanan yan bindiga.

The Nation ta rahoto cewa gwamnan ya saka wannan garabasa ne matukar bayanan suka yi dai-dai har aka kama ɗan bindiga ko aka gano maɓoyarsu.

Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo
Gwamna ya sa ladan miliyan N5m kan duk wanda ya fallasa yan bindiga a jiharsa Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Uzodinma ya bayyana haka ne yayin da ya gana da shugabannin APC na matakin jiha, kananan hukumomin da gundumomin dake faɗin jihar Imo.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta bayyana gwamnan da zata goyi baya ya gaji shugaba Buhari a 2023

Da yake jawabi a wurin taron, wanda ya gudana a fadar gwamnatinsa dake Owerri, Hope Uzodinma ya kalubalanci shugabannin APC su tashi tsaye kan ƙaruwar matsalar tsaro a jihar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wane matakin gwamnatin Uzodinma take ɗauka?

Gwamnan ya ƙara da cewa gwamnatinsa ta ɗauki matakai yanzu haka, waɗan da ake fatan za su kawo ƙarshen matsalar baki ɗaya.

Uzodinma yace:

"Mun ɗauki matakai sosai a yanzu haka, kuma muna fatan za su kawo ƙarshen matsalar yan bindiga baki ɗaya."

Bugu da ƙari, yace yan bindiga sun tafka aika-aika, amma sun gaza domin gwamnatinsa ba ta yi bacci ba.

Yace gwamnatinsa ta na aiki ba dare ba rana wajen yaƙar duhu domin haske ya samu gindin zama a jihar Imo.

A wani labarin na daban kuma Sojojin NAF sun ceto yan kasuwan da yan bindiga suka sace a hanyar Birnin Gwari-Kaduna

Kara karanta wannan

Bayan sanar da Buhari, Gwamnan APC ya bayyana dalilin da yasa zai gogayya da Tinubu a 2023

Rundunar sojin saman ƙasar nan (NAF), tace dakarunta na musamman sun kwato mutum 26 daga cikin yan kasuwan da mahara suka sace a hanyar Birnin Gwari-Kaduna.

Wannan na zuwa ne bayan wasu tsagerun yan bindiga sun sace yan kasuwa da dama a hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262