Yan Najeriya sun caccaki Garba Shehu kan rubutunsa na farko a shafin Twitter
- A ranar Laraba, gwamnatin tarayya ta sanar da ɗage hanin amfani da shafin Tuwita, bayan ƙulla yarjejeniya da kamfanin
- Garba Shehu, ya yi amfani da shafinsa wajen yaba wa yan Najeriya da kuma musu barka da zuwa, ya kuma bayyana ribar da gwamnati ta ci
- Rubutum Shehu ba su yi wa da dama daɗi ba, inda yan Najeriya suka soke shi tare da kalubalantarsa
Abuja - Wasu yan Najeriya sun yi wa hadimin shugaban ƙasa, Malam Garba Shehu, rubdugu kan rubutunsa na farko a shafin Twitter awanni kaɗan bayan dawowarta a Najeriya.
Shehu yace Najeriya ta samu ta ci riba fiye da tunani tun daga datse ayyukan shafin a Najeriya, hakan bai wa mutane daɗi ba.
Hadimin shugaban ya rubuta kamar haka:
"Barkan mu da dawowa, bari na bi sahun yan uwana yan Najeriya maza da mata wajen maraba da masalahar da aka samu tsakanin FG da kamfanin Twitter bayan samun saɓani, wanda ya yi sanadin gina tubali mai kyau da zai amfani yan Najeriya nan gaba."
"Muna yaba wa yan Najeriya musamman matasan mu masu kishi waɗan da suka yi jumurin jure wa har aka warware wannan matsala."
"Muna fatan kowane ɗan Najeriya zai yi farin ciki da samun maslaha. Ƙasar mu ce a farko. Ina mai ƙara yi wa yan Najeriya maraba."
Abinda yan Najeriya ke cewa
Da suka martani, yan Najeriya sun bukaci babban hadimin shugaban ya zayyano ribar da gwamnatin Najeriya ta samu daga matakin hana Tuwita.
Onu’kwube @RayNkah, yace:
"Barka da dawowa kace? Ko kaɗan mu ba inda muka je, ko da yaushe muna kan tuwita. Ka yi magana a karan kanka kaɗai."
Sir Ted @Deus_Ugwoke yace:
"Wane sabani kake magana a kai? Hana amfani da Tuwita da kuka yi mara amfani, mun san cewa wata manaƙisa ce ta gwamnatin APC, saboda kun ga zaɓe na matsowa kuma Tuwita na taka rawa wajen yakin neman zabe."
Oke Ayodele @infoDmedia yace:
"Lokacin gwamnatin ku a kan karagar mulki a ƙirge yake."
Cornelius Osaje @CorneliusOsaje yace:
"A yanzu kenan, ƙasa take zuwa farko, abun da takaici mutane na zuba zance ba tare da nadama ba."
Olaoye @OlaoyeOA yace:
"Kun ɗage dokar hana hawa shafin Tuwita ne sabida kun ga lokacin zaɓe ya matso."
A wani labarin na daban kuma Jaruma a Kannywood ta koka kan yadda mutane ke son ganin bayansu a kasuwancin su
Jarumar tace da kasuwanci ne suke samu suna tsira da mutuncin su, musamman idan suka daina harkar shirin fim.
Ta bayyana cewa rashin kama sana'a ke sa matan Kannywood shiga halin ƙaƙanikayi a baya, idan ta Allah tasa sun fito gidan aure.
Asali: Legit.ng