Dubu ta cika: Wani mutum ya shiga hannu yayin da ya kashe yaransa uku ya adana gawarwakinsu a cikin firinji

Dubu ta cika: Wani mutum ya shiga hannu yayin da ya kashe yaransa uku ya adana gawarwakinsu a cikin firinji

  • Rundunar yan sandan jihar Enugu ta kama wani mutumi mai suna Ifeanyi Amadikwa bisa zarginsa da kashe yaransa su uku
  • An tattaro cewa bayan ya kashe yaran nasa, sai ya saka su a cikin wani lalataccen firinji da ke gefen dakinsu
  • A halin yanzu yan sanda na ci gaba da gudanar da bincike domin gano musabbabin faruwar wannan lamari

Enugu - Rundunar yan sanda a jihar Enugu ta ce jami'anta sun kama wani mutum mai suna Ifeanyi Amadikwa kan zargin kashe yaransa da kuma adana gawarwakinsu a cikin firinji.

Hukumar yan sandan ta ce wanda ake zargin shi ne mahaifin biyu daga cikin yaran sannan ta ukun kuma 'yar matarsa ce.

Rundunar ta kuma ce mahaifiyar yaran ta barsu a karkashin kulawar wanda ake zargin a ranar 4 ga watan Janairu, inda ita kuma ta tafi kasuwa, The Cable ta rahoto.

Kara karanta wannan

Duniya kenan: Yadda aka kama wani mutum da ke cin hanjin 'yan adam a Zamfara

Dubu ta cika: Wani mutum ya shiga hannu yayin da ya kashe yaransa uku ya adana gawarwakinsu a cikin firinji
Dubu ta cika: Wani mutum ya shiga hannu yayin da ya kashe yaransa uku ya adana gawarwakinsu a cikin firinji Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Premium Times ta rahoto cewa Daniel Ndukwe, kakakin rundunar yan sandan Enugu, a wata sanarwa a ranar Laraba, 12 ga watan Janairu, ya ce a yayin neman yaran, sai aka gano su cikin firinjin dauke da raunuka.

Jawabin ya ce:

"Jami'an yan sanda da ke aiki a yankin Enugu Metro ta Jihar Enugu, a ranar 04/01/2022 da misalin karfe 1930, sun kama wani mutum mai suna Ifeanyi Amadikwa, mai shekaru 52, na gida mai lamba 74, hanyar Nkwubor, Emene, Enugu, bisa zargin kisa da kuma boye gawarwakin ‘ya’yansa mata guda uku (3) wadanda suka hada da: Chidalum Amadikwa mai shekaru 11 (wacce ta kasance diyar matarsa), Amarachi Amadikwa mai shekaru 8 da Ebubechukwu Amadikwa mai shekaru 4 a firinji da ya lalace.
"Binciken farko ya nuna cewa matar wacce ake zargi kuma mahaifiyar yaran ta je kasuwa da dansu namiji daya da suke da shi, inda ta bar sauran a hannun wanda ake zargin.

Kara karanta wannan

Yan ta'addan ISWAP su kai wani mummunan hari mutane na tsaka da Sallah a jihar Yobe

"Sai ta dawo da yammacin 04/01/2022 amma bata ga ko daya daga cikin yaran ba. Yayin da ake nemansu, sai wanda ake zargin ya ja hankalinta zuwa wajen firinjin da ya dawo da shi gida daga shagonsa a ranar 02/01/2022 wanda ya ajiye a harabar dakinsu.
"Da aka duba, sai aka gano gawarwakin yaran a cikin firinjin da alamun duka, wanda ke nuna kila an kashe su ne sannan aka adana su a cikin firinjin.
"A halin da ake ciki, an kwashi gawarwakin yaran zuwa asibiti, inda likitoci suka tabbatar da mutuwarsu, sannan an ajiye su don yin binciken sanadiyar mutuwarsu.
“Don haka, kwamishinan ‘yan sanda, CP Abubakar Lawal, fdc, yayin da yake jajanta wa uwa, ‘yan uwa da abokanan yaran da suka rasu, ya ba da tabbacin yin cikakken bincike kan lamarin tare da tabbatar da ganin cewa an yi adalci.
“Saboda haka, ya umarci mataimakin kwamishina mai kula da sashen binciken manyan laifuka na jihar da ya gudanar da cikakken bincike kan lamarin tare da tabbatar da gurfanar da duk wanda aka samu da laifi a gaban kotu.”

Kara karanta wannan

An ci gaba da shagalin biki bayan an sako amaryar da aka sace a Filato

Duniya kenan: Matashi ya yi garkuwa da yarinya 'yar shekaru 13, ya yanka ta sannan ya nemi kudin fansa a Kano

A wani labarin, wani matashi mai shekaru 21, Auwal Abdulrasheed wanda yan sandan jihar Kano suka kama ya yi bayanin yadda yayi garkuwa da wata yar talla mai shekaru 13.

Ya kuma yi bayanin yadda ya kashe ta sannan ya nemi yan uwanta su biya kudin fansa naira miliyan daya bayan ya binne gawarta a rami mai zurfi, shafin Linda Ikeji ya rahoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng