Bana zamu kawar da yunwa cikin dalibai, mun ciyar da yara milyan 9 a makarantu 53,000, Minista Sadiya

Bana zamu kawar da yunwa cikin dalibai, mun ciyar da yara milyan 9 a makarantu 53,000, Minista Sadiya

  • Hajiya Sadiya Umar Farouq ta bayyana adadin daliban da ake ciyarwa kulli yaumin a fadin tarayya
  • Yanzu kuma shirin ciyar da daliban zai samu cigaba sakamakon gudunmuwar da majalisar dinkin duniya ke shirin badawa
  • Ministar ta ce shirin ya samu karbuwa sosai a jihohin Najeriya kuma jama'a suna amfana sosai da sosai

Abuja - Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa majalisar dinkin duniya ta shirya hada kai da ita wajen inganta shirin ciyar da dalibai a makarantun firamaren Najeriya.

Ministar tallafi da jin dadin jama'a, Sadiya Umar Farouq, ta bayyana hakan a jawabin da hadimarta, Halima Oyelade, ta saki ranar Laraba a Abuja.

Hajiya Sadiya ta ce wannan sabon hadin kai da shirin abincin duniya WFP na majalisar dinkin duniya zai taimaka wajen magance matsalar yunwa cikin yara.

Tace:

Kara karanta wannan

Tallafin Survival Fund: Kano da sauran jihohin da suka fi amfana da shirin

"WFP na bada goyon baya ta hanyar bada gudunmuwar na'urorin zamani. Wannan ya hada da Tablet dake dauke da kayan abinci iri-iri - da zai taimakawa jami'an kiwon lafiya wajen zaben irin abincin ya kamata a rika girkawa."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ta hanyar wannan, za'a iya magance yunwa, talauci, rashin aikin yi dss."
"Wannan wani abu ne da Gwamnatin tarayya ke zuba kudi saboda muhimmancinshi."

Bana zamu kawar da yunwa cikin dalibai, mun ciyar da yara milyan tara, Minista Sadiya
Bana zamu kawar da yunwa cikin dalibai, mun ciyar da yara milyan tara, Minista Sadiya
Asali: Twitter

Mun ciyar da dalibai makarantu 53,000

Ministar ta kara da cewa kawo 2021, an ciyar da daliban makaranta sama milyan tara a makarantun gwamnati 53,000.

Tace wannan ya kara adadin dalibai dake zuwa makaranta a fadin tarayya.

"Yaran sun ji dadin abinci mai lafiya; wanda zai sa su cigaba da zuwa makaranta, kara mutum ilimi da karfi."

Muna ciyar da dalibai milyan 9 kulli yaumin a Najeriya, Minista Sadiya Farouq

Kara karanta wannan

Kaduna: Iyaye da malamai sun yi martani kan aikin kwana 4 na makarantun gwamnati

A baya mun kawo muku cewa Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta bayyana cewa sama da dalibai milyan tara na amfana da shirin ciyar da daliban firamare abinci watau NHGSFP.

Kamfanin dillancin labarai NAN ya ce Ministar ta bayyana hakan ne yayin taron mika kayan girki ga gwamnatin jihar Benue a LGEA Wurukum.

Ta ce an dauki masu girki sama da 100,000 a fadin tarayya.

Ministar ta baiwa al'ummar Najeriya tabbacin cewa ba za tayi kasa gwuiwa wajen tabbatar da jin dadinsu ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng