Ana sakin 'yan bindiga ba tare da hukunci ba, Gwamna Matawalle ya koka

Ana sakin 'yan bindiga ba tare da hukunci ba, Gwamna Matawalle ya koka

  • Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya ce rashin hukunta 'yan bindiga ya na daga cikin dalilan da ke assasa ta'addanci a kasar nan
  • Matawalle ya sanar da cewa, akwai babbar alaka tsakanin masu daukar nauyin Boko Haram da 'yan bindiga da ke addabar arewa ta yamma
  • Ya shawarci gwamnatin tarayya da ta samar da makamai ga dakaru sannan ta tsara yaki da 'yan ta'addan Zamfara domin daga dajikansu ake tsara sharri a arewa

Zamfara - Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya ce daga cikin dalilan da suke assasa wutar ta'addanci akwai kyale 'yan bindigar da 'yan ta'adda da ake yi babu wani hukunci.

A cewar gwamnan, sau da yawa ana sakin 'yan bindigan daji ba tare da an yi musu wani hukunci ba, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Shahrarriyar yar jarida, Kadaria Ahmed, ta shiga harkar fina-finan Nollywood

Matawalle ya sanar da hakan ne a ranar Laraba yayin da ya karba wakilan gwamnatin tarayya yayin da suka je masa ziyarar jaje kan hare-haren da aka kai wa wasu yankunan kananan hukumomin Anka da Bukkuyum a jihar.

Ana sakin 'yan bindiga ba tare da hukunci ba, Gwamna Matawalle ya koka
Ana sakin 'yan bindiga ba tare da hukunci ba, Gwamna Matawalle ya koka. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Wakilan gwamnatin tarayyan sun samu shugabancin ministan tsaro, Manjo janar Bashir Salihi Magashi mai ritaya, mai bada shawara kan tsaron shawara, Manjo Janar Babagana Munguno, Sifeta Janar na 'yan sanda, Usman Baba Alkali.

Sauran sun hada da ministan lamurran 'yan sanda, Alhaji Maigari Dingyadi, ministan walwala da jin kan 'yan kasa, Sadiya Umar Farouk da mai bada shawara na musamman ga shugaban kasa, Malam Garba Shehu.

Kamar yadda yace:

"Wata matsala da muka gano duk da kokarin dakarun sojin shi ne, basu da makaman zamani wadanda za su dinga yakin da su. Tabbatar da yakin zamani kuwa ya dogara da kayan aiki na zamani.

Kara karanta wannan

Watanni bayan mutuwar wani Mufti, Kyanwarsa taki tashi daga kan kabarinsa

"Akwai matukar amfani idan aka samar wa dakarun nan kayan yaki na zamani domin su samu nasara kan 'yan bindigan Zamfara da arewa maso yammaci."
"Alamu sun suna cewa, har sai an samar da isassun kayan aikin zamani sannan hukumomin tsaro zasu iya yakar ta'addanci yadda ya dace.
"Ana iya ganin wannan daga kiraye-kirayen da wasu shugabanni suke wa jama'arsu kan su nemi makamai domin bai wa kansu kariya.
"Al'amarin gaggawa, gwamnatin tarayya ta samar da makamai kuma ta tura su dukkan sassan kasar nan. Idan har makamai dubu za a iya samarwa, za su yi matukar amfani wurin sauya akalar yaki da 'yan bindiga a cikin kankanin lokaci da izinin Allah.
"Ina son janyo hankalin gwamnatin tarayya kan cewa, asusan da ke daukar nauyin ta'addanci a sassan arewa suna da alaka. A wasu misali, akwai shaidar cewa akwai alaka tsakanin Boko Haram da wasu kungiyoyin ta'addanci na arewa maso yamma.

Kara karanta wannan

Kashe-kashen jihar Zamfara ba zai tafi a banza ba, in ji APC

"Ina son karawa da cewa, duk wani tsari da za a fitar na yaki da 'yan bindiga da duk wasu nauyin ta'addanci, ya mayar da hankali a jihar Zamfara. Dajikanmu sun zama madaddalar 'yan bindiga wanda daga nan suke shiryawa tare da kaddamar da farmaki a sauran sassan arewa maso yammaci," ya kara da cewa.

Rundunar sojin Najeriya ta musanta hannun jami'anta a fada da masu hako zinari a Katsina

A wani labari na daban, rundunar sojin Najeriya ta musanta zargin da ake wa jami'anta na yin musayar wuta duk saboda zinare a kauyen Magama da ke karamar hukumar Jibia a jihar Katsina.

Darektan hulda da jama’an rundunar, Onyeama Nwachukwu, ya musanta zargin ta wata takarda ta ranar Lahadi a Abuja, Daily Nigerian ta ruwaito.

Mr Nwachukwu ya ce an fara sakin wasu labarai a kan yadda wasu sojoji suka amince a ba su N500,000 ga kowanne dunkulen zinare daga masu hako su, bayan lamarin ya sauya inda su ka gano cewa masu hakar zinaren sun samo manyan dunkulai na zinare, yarjejeniyar ta tashi.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Jerin farmaki 5 da suka tada hankalin 'yan arewa a 2021

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng