Cire tallafin man fetur: Ku kasance cikin shirin yin zanga-zanga, NLC ga mambobinta
- Kungiyar kwadago ta kasa ta umarci duk mambobinta, kungiyoyin da ke karkashinta da sauran ma’aikatan gwamnati da su shirya fara zanga-zanga ranar 27 ga watan Janairu da 1 ga watan Fabrairu saboda cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ke shirin yi
- Wannan shi ne babban dalilin da yasa shugabannin ma’aikatun gwamnati wanda shugaban NLC, Ayuka Wabba ya jagoranta su ka shirya taro na musamman a gidan kwadago da ke Abuja ranar Talata
- Wani mamban kwamitin ayyukan kungiyar wanda ya sakaya sunansa ya ce shugabanni da duk wasu sakatare janar na kungiyoyin da ke karkashin NLC sun lashi takobin sa mammabobinsu yin zanga-zangar
Abuja - Kungiyar kwadagon Najeriya, ta umarci mambobinta, kungiyoyin da ke karkashinta da sauran ma’aikatan gwamnati su shirya yin zanga-zangar da za a yi a fadin kasa daga ranar 27 ga watan Janairu zuwa 1 ga watan Fabrairu kan shirin gwamnatin tarayya na cire tallafin man fetur.
Kungiyar ta bukaci duk kungiyoyin da ke karkashinta a fadin kasar nan da su umarci mambobinsu don tabbatar da zanga-zangar da za a yi ta kasa baki daya, The Punch ta ruwaito.
Wannan shi ne babban dalilin yin taron wanda shugaban NLC, Ayuba Wabba, ya yi da shugabannin kungiyoyin da ke karkashin Kungiyar kwadagon a gida da ke Abuja ranar Talata.
Wani mamban kwamitin ayyuka kamar yadda The Punch ta shaida, wanda ya bukaci a sakaya sunansa ya ce duk wani shugaba ko sakatare janar na kungiyoyin da ke karkashin NLC ya lashi takobin sa mambobinsu yin zanga-zangar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Suna son mambobin NLC da yawa su fito zanga-zangar
Shugaban NLC ya kada baki ya ce:
“An bukaci mu je mu shirya mambobinmu da ke kasar nan don tabbatar da zanga-zangar da ake shiryawa a ranar 27 ga watan Janairu.
“An umarci ko wacce kungiya da ta shiryo mambobinta masu yawa don yin zanga-zangar hakan zai sa a fi fahimtar mu. Muna bukatar mutane da yawa wurin zanga-zangar.
“Ko wanne shugaba da sakatare janar na ko wacce kungiya ya lashi takobin tattaro mambobin da ke karkashinsa don zanga-zangar. Yanzu haka CSO su na aiki da kungiyar kwadago. Kuma su na ba mu goyon baya a kan zanga-zangar da mu ke shirin yi ranar 27 ga watan Janairu.”
Wabba ya ce ba zasu zura ido a cire tallafin mai suna kallo ba
A cewarsa kungiyar ba za ta zura ido tana kallo a cire tallafin kudin mai ba inda ya kara da cewa:
“Idan hakan ta faru, bala’i ya same mu a kasar nan.”
Tun a shekarar da ta gabata gwamnatin tarayya ta bayyana shirinta na cire kudin tallafin man fetur cikin watanni ukun farkon shekarar nan.
Turawan Mulkin Mallaka Suka Ƙirƙiri Bikin New Year, MURIC Ta Ce Buhari Ya Dena Bada Hutun Ranar 1st January
A wani labarin, Kungiyar kare hakkin musulmai, MURIC ta bukaci gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi gyara a kan hutun da ta ke bayarwa, ta mayar da daya ga watan Muharram na shekarar musulunci a matsayin ranar hutu, NewsWireNGR ta ruwaito.
Kungiyar ta zargi shugaban kasa Muhammadu Buhari da bayar da hadin-kai wurin mayar da Najeriya kasar kiristoci inda ake kyale bukukuwan musulunci a bayar da hutu a lokacin na kiristoci.
Kamar yadda takardar wacce darektan MURIC ya saki, Farfesa Ishaq Akintola, ya saki, kungiyar ta zargi yin shagulgulan bikin sabuwar shekarar kiristoci a matsayin rashin adalci ga musulman Najeriya kuma hakan bai yi daidai da demokradiyya ba.
Asali: Legit.ng