Daga karshe: An sako shugaban ASUU da tsohon dan takarar gwamna da aka sace
- Wasu masu garkuwa da mutane sun sako shugaban ASUU reshen jihar Filato da suka sace kwanakin baya
- Hakazalika, sun kuma sako wani tsohon dan takarar gwamnan jihar da aka sace su tare da shugaban na ASUU
- Rahotanni sun ce an biya kudaden fansa kafin a sako su kamar yadda masu garkuwar suka nema a farko
Jihar Filato - Rahoton Premium Times ya ce, masu garkuwa da mutane sun sako shugaban kungiyar malaman jami’o’i (ASUU), reshen jami’ar jihar Filato, Hassan Zitta, da tsohon dan takarar gwamna a jihar, Nicholas Nshe.
Sakataren kungiyar, Samson Deme ne ya tabbatar da hakan ga jaridar ta wayar tarho, ya ce an sako mutanen biyu ne a daren ranar Talata bayan sun shafe kwanaki 11 a wurin masu garkuwa da mutane.
Mista Deme ya kara da cewa, akalla an biya kudin fansa naira miliyan 10 kafin a sako su.
A baya Punch ta rahoto cewa masu garkuwa da mutanen, sun yi watsi da kudi N7m a matsayin kudin fansan Nshe.
Mutanen biyu sun shafe kwanaki 11 tare da wadanda suka sace su bayan an yi garkuwa da su a jajibirin sabuwar shekara a gidan tsohon dan takarar gwamna kuma tsohon shugaban karamar hukumar Shendam, Mista Nshe.
Mista Deme ya ce:
“Yayan ya ce bayan an biya Naira miliyan 10 ba a sake su ba. Sai da suka kara wasu kudi domin a sake su amma ban san nawa ba."
An samu labarin cewa masu garkuwan sun bukaci kimanin Naira miliyan 90 – Naira miliyan 50 ga tsohon dan takarar gwamnan da kuma Naira miliyan 40 ga shugaban ASUU domin a sako su.
Ya zuwa yanzu dai ba a samu jin ta bakin Ubah Ogaba, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Filato ba.
‘Yan bindiga sun yi garkuwa da wani dan jarida, Salisu Maki, a Nasarawa
A wani labarin, wasu ‘yan bindiga wadanda sun kai 9 a ranar Talata, sun yi garkuwa da wani dan jarida wanda ma’aikaci ne da Nasarawa Broadcasting Service, Salisu Maki a Lafia, babban birnin jihar, Vanguard ta ruwaito.
Sun sace Maki ne da misalin karfe 9:30 na safiyar Talata a gidansa da ke kan titin Akurba a karamar hukumar Lafia yayin da ya ke hanyarsa ta komawa gida daga aiki.
Ganau sun shaida yadda ‘yan bindigan su ka afka har wuraren gidan Maki su na harbe-harbe inda su ka tsorata jama’a daga nan su ka yi garkuwa da mutumin.
Asali: Legit.ng