Tashin Hankali: Kotu ta yanke wa matashi dan shekara 35 hukuncin kisa a Ibadan

Tashin Hankali: Kotu ta yanke wa matashi dan shekara 35 hukuncin kisa a Ibadan

  • Wata kotu dake zamanta a Ibadan, babban birnin jihar Oyo, ta kama wani matashi ɗan shekara 35. Oriyomi Felix, da laifin fashi da makami
  • Alkalin kotun, mai shari'a Bayo Taiwo, yace lauya mai gabatar da ƙara ta kawo hujjoji kwarara, dan haka ya yanke masa hukuncin kisa
  • Rahotanni sun bayyana cewa Felix ya jima yana wannan aika-aika, kuma ya taba bindige wani mai suna Nurudeen

Ibadan - Babbar kotun jihar Oyo dake zamanta a Ibadan, ta yanke wa matashi dan shekara 35, Oriyomi Felix, hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan kama shi da laifin fashi da makami.

Matashin ya fuskanci shari'a kan tuhuma biyu, haɗa manaƙisa da kuma fashi da makami, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gwamnatina ba za ta yi watsi da ku ba: Shugaba Buhari ya yi jajen kisan 'yan Zamfara

Alƙalin kotu, Mai shari'a Bayo Taiwo, wanda ya yanke wannan hukuncin ranar Litinin, yace mai shigar da ƙarar, Mista Sandra Stella, ta tabbatar da zargin da ake wa Felex, da hujjoji masu ƙarfi.

Kotu a Ibadan
Tashin Hankali: Kotu ta yanke wa matashi dan shekara 35 hukuncin kisa a Ibadan Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Alƙalin yace wanda ake zargi da sauran yan tawagarsa sun aikata laifin fashi kan mutane da dama a ranar 12 ga watan Disamba, 2017, a Tose Moniya, dake shiyyar Ibukun Oluwa, Ibadan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ƙara da cewa yan fashin sun yi amfani da bindigu wajen aikata wannan aika-aika kan Kamorudeen Adeyemi, Ibrahim Sariyu, Alhaji Alowonle Nurudeen da sauransu.

Shin ya kashe wani ne yayin sata?

Mista Taiwo, yace an gabatar masa da kwararan shedun da suka tabbatar da cewa wanda ake ƙara ya yi wa waɗan nan mutanen fashi har ya harbi Nurudeen.

Alkalin yace:

"Saboda haka, na tabbatar wanda ake ƙara ya aikata abin da ake tuhumarsa a kai, kuma kotu ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya."

Kara karanta wannan

Magidanci ya lakadawa budurwa dukan tsiya, ya umarci matansa su kashe ta a jihar Kano

Yadda shari'ar ta kasance

Lauya mai gabatar da ƙara ta shaida wa kotun cewa mutumin ya jima yana aikata fashi da makami tare da sauran yan tawagar su lokaci bayan lokaci a yankin Tose Moniya II kafin dubunsa ta cika a 2017.

Stella, mataimakiyar darakta a ma'aikatar shari'a ta jihar Oyo, tace mutumin ɗauke da makamai, ya sace kayan al'umma ta suka haɗa da na'ura mai kwakwalwa, wayoyin hannu, sarkokin mata da tsabar kudi.

A wani labarin kuma Atiku ya aike da muhimmin sako ga hukumomin tsaro kan kisan mutum 20 a Zamfara

Atiku Abubakar ya jajantawa al'umma da gwamnatin jihar Zamfara bisa kisan gillan da yan bindiga suka yi wa mutane a jihar kwanan nan

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa karkashin PDP ya kuma yi kira ga jami'an tsaron ƙasar nan su kara matsa ƙaimi wajen kawo karshen yan ta'adda a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262