Rundunar sojin Najeriya ta musanta hannun jami'anta a fada da masu hako zinari a Katsina

Rundunar sojin Najeriya ta musanta hannun jami'anta a fada da masu hako zinari a Katsina

  • Rundunar sojin Najeriya ta musanta zargin da ake yi wa sojoji na musayar wuta bayan wata hayaniya ta shiga tsakaninsu a kan zinare a kauyen Magama
  • Kakakin rundunar sojin, Onyema Nwachukwu ya musanta zargin ta wata takardar da ya saki ranar Lahadi a Abuja
  • Ya ce labarin ba yi da tushe balle makama kuma wasu ne su ka zauna tare da shirya labarin na kanzon kurege duk don zubar da mutuncin sojoji

FCT, Abuja - Rundunar sojin Najeriya ta musanta zargin da ake wa jami'anta na yin musayar wuta duk saboda zinare a kauyen Magama da ke karamar hukumar Jibia a jihar Katsina.

Darektan hulda da jama’an rundunar, Onyeama Nwachukwu, ya musanta zargin ta wata takarda ta ranar Lahadi a Abuja, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan sanda sun shiga tsakani yayin da kwarto ya kashe mijin daduronsa

Rundunar sojin Najeriya ta musanta hannun jami'anta a fada da masu hako zinari a Katsina
Rundunar sojin Najeriya ta musanta hannun jami'anta a fada da masu hako zinari a Katsina. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

Mr Nwachukwu ya ce an fara sakin wasu labarai a kan yadda wasu sojoji suka amince a ba su N500,000 ga kowanne dunkulen zinare daga masu hako su, bayan lamarin ya sauya inda su ka gano cewa masu hakar zinaren sun samo manyan dunkulai na zinare, yarjejeniyar ta tashi.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, a cewarsa labarin na kanzon kurege ne, don ba yi da tushe balle makama, kawai wanda ya rubuta shi ya wallafa ne don bata sunan sojojin Najeriya.

Kamar yadda yace, babu wani soja da ya mutu ko kuma rikicin ya hada shi da masu hakon zinare ba bisa ka’ida ba a kauyen Magama ranar 5 ga watan Janairu.

“Ba gaskiya bane labarin da ya yadu a yanar gizo, sojojin da aka tura yankin arewa maso yamma jajirtattu ne a kan yaki da ta’addanci da sauran miyagun ayyuka a yankin.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da direban mota tare da fasinjoji 4 a Abuja

“Ba a basu damar shiga harkallar hako zinare ta halastacciyar hanya ko ta akasin ta ba.
“Sharri, suka da kirkirar labaran bogi ba su bane ababen da rundunar take bukata ba a halin yanzu da suke cikin tsanani,” a cewarsa.

Mr Nwachukwu ya bukaci jama’a su daina yarda da labaran kanzon kuregen da su ke da alaka da rundunar sojin Najeriya wadanda su ka dage wurin kawo zaman lafiya da tsaro a yankin arewa maso yamma.

Ya kara tabbatar wa gaba daya jama’a a kan jajircewar da sojoji su ke yi na kawo tsaro da kuma karshen ta’addanci a arewa maso yamma.

An tura sojoji yaki a Katsina sun koma hada kai da masu hakar ma'adinai, matsala ta bullo

A wani labari na daban, sojoji biyu da masu hakar ma'adinai bakwai sun mutu bayan wata arangama da suka yi kan wani tarin gwal da aka gano a garin Magama dake kan iyaka a karamar hukumar Jibiya ta jihar Katsina.

Kara karanta wannan

Hedkwatar Tsaro ta ja kunnen ‘yan siyasa da sauran jama’a kan amfani kayan sojoji

Jaridar Daily Nigerian ta rawaito cewa rikicin ya afku ne a ranar Laraba da misalin karfe 6 na yamma bayan da aka gano gwal din daga cikin wani rami da masu aikin hakar ma’adinan suka tona.

Kimanin mutane 40, masu hakar ma’adinan ba bisa ka’ida ba, wadanda kuma ke dauke da makamai, sun biya sojojin N500,000 kan kowanne rami kafin a barsu su fara aikin hakar ma’adinan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: