Dalla-Dalla: Yadda FG ta kashe N56.9bn kan mata da matasan Najeriya a 2021

Dalla-Dalla: Yadda FG ta kashe N56.9bn kan mata da matasan Najeriya a 2021

  • Bincike ya bayyana cewa, N577 biliyan gwamnatin tarayya ta kashe wurin inganta rayukan mata da matasan Najeriya a 2021
  • Kamar yadda aka gano, an bai wa matan da matasa tallafin jari na kudi, injinan nika da na saka tare da horar da su ayyukan hannu
  • Wannan kudaden an raba su har sau 763 domin tsamo mata da matasan birane da karkara daga talauci da kangin rayuwa

A kalla N57 biliyan gwamnatin tarayya ta kashe kan mata da matasan Najeriya a shekarar 2021, binciken Nigerian Tribune ya bayyana.

Kwamitin farfado da tattalin arzikin ya ware makuden kudade domin tsamo matan Najeriya da ke birane da kauyuka daga talauci.

Dalla-Dalla: Yadda FG ta kashe N56.9bn kan mata da matasan Najeriya a 2021
Dalla-Dalla: Yadda FG ta kashe N56.9bn kan mata da matasan Najeriya a 2021. Hoto daga tribuneonlineng.com
Asali: UGC

Kamar yadda ministan kudi, kasafi da tattalin arziki, Zainab Ahmed tace a watan Nuwamban 2021, N3.40 tiriliyan aka kashe a wurin bayar da jari.

Kara karanta wannan

Duk da yawaitar kashe-kashe, Shugaban ma'aikatan tsaro ya yi iƙirarin kalubalen ya ragu

"Daga ciki, N2.98 tirilan ya wakilci kashi 83 na tanadin da aka yi wa ma'aikatu da cibiyoyin gwamnati," kasafin ya nuna.

Ahmed ta sanar da hakan a yayin gabatar da kasafin kudin 2022 na gwamnatin tarayya da aka amince da shi, Nigerian Tribune ta ruwaito.

A tallafin da aka raba a fadin kasar nan, kasafin shi ne kashi na 763 na tallafin mata da matasa wanda ya hada da kyautar kudi, siyan injinan dinki da na nika, siyan na'ura mai kwakwalwa, koyar da sana'o'i a fannoni daban-daban da kuma kasuwanci tare da siyan sutura ga mata zalla da kananan yara.

Binciken Nigerian Tribune ya bayyana cewa, an kashe N18,233,926,583 wanda aka sadaukar domin horar da mata a sassan kasar nan.

Kara karanta wannan

Bamu yarda da sanya haraji kan lemun kwalba ba, NLC ga Gwamnatin tarayya

Bincike ya bayyana cewa, kusan N1,960,000,000 aka siya injin nika, N6,460,858,913 aka kashe wurin koyar da sana'o'i domin mata da matasa a kasar nan.

2023: Ku samu katikan zaben domin zaben shugabanni nagari, Sanusi

A wani labari na daban, Muhammad Sunusi II, shugaban kungiyar Tijjaniyya ta kasa, ya shawarci duk wani dan kasar da shekarunsa su ka kai, ya tanadi katin zabensa kafin shekarar 2023.

Sunusi ya yi wannan furucin ne a ranar Asabar yayin taron zagayowar bikin maulidi na duniya da su ka yi a Lokoja, jihar Kogi, TheCable.ng ta ruwaito.

Tsohon sarkin Kano ya ce duk wani dan Tijjaniyya ya zage damtse a harkar siyasa, inda yace ko wanne dan Najeriya ya dage ya yi zabe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng