Ku bayyana maboyar 'yan bindiga, Babban limamin Masallacin kasa ga 'yan Najeriya

Ku bayyana maboyar 'yan bindiga, Babban limamin Masallacin kasa ga 'yan Najeriya

  • Babban limamin masallacin kasa da ke Abuja, Dr Muhammad Kabir Adam a ranar Juma’a ya bukaci ‘yan Najeriya su bayyana maboyar ‘yan bindiga da duk wasu ‘yan ta’adda
  • Malamin ya ce yin hakan ne zai taimaka wa sojoji da sauran jami’an tsaro wurin yaki da ta’addancin da ya addabi kasar nan
  • Ya yi wannan kiran ne yayin tattaunawa da manema labaran soji jim kadan bayan kammala addu’o’i na musamman ga mazan jiya bayan kammala sallar Juma’a

FCT, Abuja - Babban limamin masallacin kasa da ke Abuja, Dr Muhammad Kabir Adam, a ranar Juma’a ya bukaci ‘yan Najeriya da su dinga bayyana maboyar ‘yan bindiga, ‘yan ta’adda, masu garkuwa da mutane da saura miyagun mutanen da su ka addabi kasar nan.

Malamin ya ce hakan zai taimaka wa sojoji da sauran jami’an tsaro wurin yaki da ta’addanci.

Kara karanta wannan

Nasara daga Allah: An kashe 'yan Boko Haram 950, 24,059 sun mika wuya a kasa da watanni 7

Ku bayyana maboyar 'yan bindiga, Babban limamin Masallacin kasa ga 'yan Najeriya
Ku bayyana maboyar 'yan bindiga, Babban limamin Masallacin kasa ga 'yan Najeriya. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Daily Trust ta ruwaito cewa, Dr Adam ya yi wannan furucin ne yayin tattaunawa da manema labaran sojoji bayan kammala addu’o’i na musamman ranar Juma’a don tuna mazan jiya a shekarar 2022.

“Ina kira ga ‘yan Najeriya akan kawo bayanai masu muhimmanci wadanda zasu taimaka wurin gano maboyar ‘yan ta’adda a duk inda suke. Wannan zai zama kamar bayar da hadin kai ga sojojinmu duk da wannan mummunan yanayin da mu ka tsinci kawunanmu amma ya kamata mu yi hakan don su yi ayyukansu yadda ya dace,” a cewar malamin.

Dr Adam ya bayyana cewa an yi addu’o’in ne na ranar Juma’a don tunawa da mazan jiya wadanda su ka sadaukar da rayuwarsu wurin ganin sun dawo da darajar kasa da kuma samar da tsaro da zaman lafiya ga kasarsu.

Kara karanta wannan

Daga Karshe: Gwamnati Buhari amince da ayyana 'yan bindiga a matsayin 'yan ta'adda

Ya kara da cewa, “An yi addu’o’in da hudubar ne don nusar da ‘yan Najeriya muhimmancin yi wa jami’an tsaro addu’ar samun nasara don cin nasara a duk da kalubalen da ake fuskanta.
“Sannan kuma hudubar za ta taimaka wa ‘yan Najeriya wurin tuba da yin abubuwan da su ka dace da rayuwarsu don Allah cikin rahamarsa ya dube mu kuma ya kawo mana karshen rashin tsaron da Najeriya ke fuskanta.
“Nasararsu nasarar mu ce. Don haka muna fatan Ubangiji ya kara wa jami’an tsaro kwarin guiwa kuma ya ci gaba da taimakon shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya kara masa lafiya da fasahar ci gaba da shugabantar kasar nan.”

Kungiya ga Ortom: Ka mayar da hankali wurin biyan albashi a Benue, maimakon matsawa Buhari

A wani labari na daban, kungiyar matasan Tiv ta fadin duniya ta yi kira ga gwamna Samuel Ortom na jihar Benue da ya mayar da hankali wurin dawo da sunansa da bunkasa walwalar ma'aikata a jihar fiye da "amfani da sunan shugaban kasa Muhammadu Buhari a kanun labarai".

Kara karanta wannan

'Dan Sanda Abokin Kowa: Lokuta 4 da ƴan sandan Najeriya suka yi wa mutanen da basu sani ba manyan abin alheri

Shugaban kungiyar matasan Tiv, Honarabul Mike Msuaan, ya fadi hakan ne yayin mayar da martani ga amsar da Ortom ya bawa shugaban kasa Muhammadu Buhari bayan tattaunawa da ChannelsTV.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng