Zan yi rikici da duk wanda ya gayyaceni kotu amsa wani tambaya bayan na bar Ofis, Buhari
- Shugaba Buhari yace kada wanda ya kirasa kotu wani bayani ko amsa tambayaidan ya bar mulki a shekarar 2023
- Manyan lauyoyin Najeriya sun ce wannan babatu ne kawai, wajibi ne a kirasa yayi bayani kan abubuwan da yayi
- Kungiyoyin fafutuka sunce ai ya zama dole Shugaba Buhari ya yi hisabin ayyukansa idan ya bar mulki
Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari ya yi gargadin cewa kada wani ya gayyacesa kotu amsa wasu tambayoyi kan yadda yayi mulki bayan ya bar Ofis a 2023.
Buhari yace duk wanda ya gayyacesa za suyi rikici saboda duk abinda suke bukata na rubuce a kasa.
Ya bayyana hakan ne a hirar da yayi da gidan talabijin Channels ranar Laraba.
Yayinda yan jaridan Channels suka tambayesa shin ya nada matsala da wanda za gajesa, Buhari yace:
"A'a, ko waye yazi. Komai na rubuce. Kada wanda ya kirani kotu gabatar da wani hujja, idan ba haka ba, zamu yi rikici saboda komai na rubuce. Na tabbatar da hakan."
Manyan lauyoyi sun caccaki Buhari bisa wannan magana
Manyan lauyoyi a Najeriya, kungiyoyin yan fafutuka da jam'iyyar hamayya PDP sun caccaki Shugaba Buhari bisa wannan magana da yayi.
A cewarsu, Shugaba Buhari ya shirya tsaf don amsa tambayoyi kan abubuwan da yayi idan ya sauka daga mulki a 2023.
Punch ta ruwaito manyan lauyoyi irinsu Femi Falana, Mr Ifedayo Adedipe, Mr Mike Ozekhome da Mr Ebun-Olu Adegboruwa, da cewa kundin tsarin mulki bata baiwa tsaffin Shugabannin kasa kariya ba, kuma wajibi ne Buhari ya shirya amsa tambayoyi.
Kungiyoyin fafutuka su caccaki Buhari
Mataimakin shugaban kungiyar SERAP, Kolawole Oluwadare, ya ce sashen 308(1)(3) na kundin tsarin mulkin Najeriya bai baiwa gwamna ko shugaban kasa kariya ba idan suka sauka.
Ya ce abinda ya faru da tsohon Shugaban kasar Afrika ta kudu, Jacob Zuma, bayan ya bar ofis darasi ne ga Najeriya.
Hakazalika shugaban gamayyar kare demokradiyya da kundin tsarin mulkin Najeriya, Ariyo-Dare Atoye, ya ce wajibi ne Shugaban kasa yayi hisabi bayan ya bar mulki ko ya so, ko ya ki.
Yace:
"Abu biyu Shugaban kasa ke kokarin yi. Na farko yana gudun yin hisabi da daukan nauyi. Abu daya zamu fada masa shine yayi nasa babatun amma samun mun tursasashi hisabin ayyukansa."
Asali: Legit.ng