Bamu yarda da sanya haraji kan lemun kwalba ba, NLC ga Gwamnatin tarayya

Bamu yarda da sanya haraji kan lemun kwalba ba, NLC ga Gwamnatin tarayya

  • Kungiyar yan gwagwarmaya NLC tace sam ba zata amince da sabon haraji kan lemun kwalba ba
  • NLC tace dan lemun kwalba da burodi da talaka ke amfani wajen gusar da yunwa yanzu ana kokarin kara farashin
  • Kungiyar masana'antun Najeriya tayi tsokaci kan shirin da gwamnati keyi na kakaba kudin haraji kan kayan zaki

Abuja - Kungiyar Kwadagon Najeriya (NLC) ta bayyanawa gwamnatin tarayya cewa ba za ta yarda da karin kudin harajin N10/lita da take shirin kakabawa masana'antun lemun kwaba ba.

NLC ta bayyana matsayarta ne a jawabin da Shugabanta na kasa, Ayuba Wabba, ya sake ranar Juma'a a Abuja.

Gwamnatin tarayya ta sanar da karin kudin harajin N10 ga litan dukkan lemukan kwalba marasa bugarwa.

Ministar Kudi, Kasafin Kudi, da shirye-shiryen tarayya, Hajiya Zainab Shamsuna Ahmed, ta bayyana cewa an yi wannan kari ne don hana mutane shan kayan kwalba irinsu Coca-Cola, Pepsi, Sprite, dss saboda yawaitan cututukan dake da alaka da Siga irinsu kiba da ciwon siga.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun sace wani shugaban kwastam mai ritaya a gonarsa a Kwara

Shugaban NLC Wabba ya ce kara wannan kudin haraji zai kara tsananta halin da yan Najeriya ke ciki na kunci da wahala.

Saboda haka ya yi kira ga majalisar dokokin tarayya tayi gaggawa gyara dokar dake kokarin kakaba wannan haraji.

Gwamnatin tarayya
Bamu yarda da sanya haraji kan lemun kwalba ba, NLC ga Gwamnatin tarayya
Asali: Twitter

A cewarsa:

"Kungiyar ta gabatar da dalilan masu karfi na rashin amincewarta da gwamnati kan wannan sabon haraji kan kayan zaki. Daya daga cikin dalilan shine wannan zai tsananta halin da talakan Najeriya ke ciki saboda da kwalban lemu guda da biredi ya gusar da yunwa."
"Abin damuwa shine za'a shiga halin yunwa idan farashin lemun kwalba ya tashi sakamakon kudin harajin kuma yan Najeriya da dama zasu gaza saya."

Talakawan Najeriya zasu ji jiki, Masana'antun lemu sun gargadi Gwamnati

Kungiyar masana'antun Najeriya watau MAN ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta sake tunani kan shirin sanya harajin N10 ga litan lemun kwalba da kayan zaki marasa bugarwa.

Kara karanta wannan

Harajin N10 kan lemun kwalba: Talakawan Najeriya zasu ji jiki, Masana'antun lemu sun gargadi Gwamnati

MAN ta bayyana hakana jawabin da kaddamar inda tace wannan doka na gwamnati asara zai haifar mata ba riba ba, rahoton ThisDay.

A cewar MAN, daga yanzu zuwa 2025, gwamnatin tarayya na iya samun harajin N81bn amma ta rasa N197bn na wasu harajin daban irinsu VAT da CIT daga wajen kamfanonin lemu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng