Shugaba Buhari, Gwamnoni, Ministoci sun yi ta'aziyyar Sheikh Ahmad Bamba
- Shugaban kasa, Gwamnan Kano, Gwamnan Bauchi, Ministan Sadarwa da sauran su sun yi alhinin rashin Sheikh Ahmad BUK
- Daruruwan mutane sun halarci Sallar Jana'iza tare da birne babban malamin addinin
- Sallar Jana'izarsa ta gudana ne a masallacin Darul Hadith bayan Sallar Juma'a a jihar Kano
Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari, a ranar Juma'a, ya aike sakon ta'aziyyarsa ga al'ummar Musulmi bisa mutuwar Shehin Malami, Dr Ahmad Muhammad Ibrahim.
Shugaba Buhari yace za'a rika tunawa da Dr Ahmad Muhammad Bamba bisa gudunmuwar da ya baiwa addinin Musulunci da Najeriya da kuma soyayyarsa ga karantar da al'umma.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu ya bayyana sakon Buhari a jawabin da ya saki ranar Juma'a.
Buhari yace:
"Lallai labari ne mai ban takaici muka samu na rasuwar Dr Ahmad. Mutum ne mai riko da addini kuma ya sadaukar da rayuwarsa bisa ilmin addini. Muna aike sakon ta'aziyya kuma muna addu'a Allah ya jikansa."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Gwamna Ganduje ya yi Alhinin mutuwarsa
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Kano ya bayyana mutuwar Dr Ahmad Bamba a matsayin babban rashi ga al'ummar jihar.
Ganduje ya siffantashi a matsayin mai kwadaitar da zaman lafiya cikin al'umma.
Sakataren yada labaran gwamnan, Abba Anwar, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki.
Gwamna Bala na Bauchi ya aike sakon ta'azziyarsa
Gwamna Bala Abdulkadir Mohammad na Bauchi ya yi alhinin mutuwar Dr Ahmad Bamba.
Yace rasuwar babban malamin addinin musulunci, kuma masanin Hadisi ta haifar da babban giɓi da tabo a zukatan al'umar musulmin Najeriya, Afrika da duniya baki ɗaya.
Yace:
"Tsawon rayuwarsa, shehin malamin ya karantar da al'uma ilimin Hadisan fiyayyen halitta Annabi Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, a madadin gwamnati da al'umar jihar Bauchi, ina miƙa saƙon ta'aziya ga iyalen marigayin, masarauta da gwamnatin jihar Kano,Jami'ar Bayero ta Kano, zauren Darul hadis da ɗaukacin musulmi.
Allah ya haskaka kabarin sa ya kyautata bayan sa."
Ministan Sadarwa, Dr Isa Ali Pantami ya yi alhini
Malamin addini kuma Ministan Sadarwa da tattalin arzikin zamani ya yi addu'an Allah ya gafartawa Sheikh Ahmad Muhammad BUK.
Pantami yace ko mako guda ba'a yi ba suka hadu a Kano wajen kaddamar da littafin Hadisi da Malamin ya wallafa.
Yace:
Allah Ya gafartawa Malaminmu, Dr Shaykh AlMuhaddith Ahmad Muhammad Ibrahim (Dr Ahmad BUK).
A ranar Asabar, 1 ga Rabiuth-Thani 1443, muna Kano tare da sauran malamanmu da shuwagabanni wajen kaddamar da Fassarar littafinsa na Muwatta Malik, da Alhaji Ibrahim Muhammad Gerawa Ya dauki nauyin bugawa.
Allah Ya gafarta masa, Ya jikan sa, Ya jikan iyayenmu, da malamanmu, da 'ya'yanmu, Ya kyautata namu bayan na su.
Allah Ya gafartama dukkanmu,
Asali: Legit.ng