Babbar Magana: Tashin hankali yayin da gawa ta yi batan dabo a dakin ajiye gawa ranar biso
- Hankula sun tashi yayin da gawar wata mata ta yi batan dabo a dakin ajiye gawa a ranar da za a binne ta
- An tattaro cewa tun bayan da yan'uwan marigayiyar suka ajiye gawarta a dakin ajiye gawar sai masu tsaron wajen suka ki bari su ganta
- Asiri ya tonu ne lokacin da aka karbo gawar domin biso kawai sai aka ga wata daban
Ebonyi - Yan uwar wata mata da ta kwanta dama sun shiga halin tashin hankali yayin da gawar matar ta yi batan dabo a dakin ajiye gawa a jihar Ebonyi.
Ba a samu damar yin bikin binne gawar ba sakamakon batan gawar, jaridar The Nation ta rahoto.
A cewar rahoton, an ajiye gawar marigayiya Madam Grace Orjiokoro a dakin ajiye gawa na babban asibitin Owutu Edda a karamar hukumar Afikpo ta kudu da ke jihar bayan ta mutu a asibitin. Ta mutu tana da shekaru 80 a duniya a watan Yulin 2021.
Masu zaman makoki da yan uwa sun taru a gidan marigayiyar suna ta wake-wake kawai sai labarin batan gawar ya iso masu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wani dan uwar marigayiyar, Fred Okoro, ya ce ya kadu matuka lokacin da iyalan suka je karbar gawar yar'uwarsu a ranar biso, kawai sai aka ga gawar wata da daban.
Ya ce sun yi zargin akwai wani abu a kasa wata daya da ya gabata bayan sun ajiye gawa a dakin ajiye gawar.
Duk kokarin da iyalan suka yi don ganin halin da gawar ke ciki ya ci tura domin masu ajiye gawar na ta ikirarin cewa ana tsaftace dakin ajiyar gawar.
Fasto Okoro ya ce komai ya bude lokacin da iyalan suka je wajen ajiye gawar don karbar gawar domin biso, kawai sai suka ga an gabatar masu da gawar wata daban.
Ya ce:
"Gawar da aka gabatar mana ba namu bane saboda yar'uwata doguwa ce, tsawonta ya kai sahu 6 amma sai muka gano cewa wannan gajeruwa ce.
"Ba ma wannan ba, kitson da ke kan yar'uwata ya bazu a kafadarta a lokacin da ta mutu amma wannan aski ne a kanta."
Wata diyar marigayin, wacce ta kasance jami'ar sojin ruwa, Welsie Okoro, ta bayyana lamarin a matsayin abun al'ajabi.
Ta bayyana cewa a lokacin da suka kai masu ajiyar gawar ofishin yan sandan Owutu, sun yi ikirarin cewa sun yi kuskure wajen mika gawar mahaifiyarta ga wani iyali don binnewa.
Ta ce:
"Kuma hatta ga mai tsaron dakin ajiyar gawar Mista Felix ya ce wani abokin aikinsa ya ce ya san mutumin da ya baiwa gawar mama."
Fasto Okoro ya ce yana zargin rashin gaskiya a lamarin saboda wadanda ake zargin sun yi musayar gawar yar'uwarsa sun karyata zargin.
Ya ce:
Ikon Allah: Yadda raken N50 ya jawo rikicin da ya kai ga zub da jini da garkame kasuwa a jihar Kwara
"An gano cewa mutanen sun ajiye gawar ne a watan Mayu yayin da aka ajiye kanwata a ranar 2 ga Yuli."
A ruwayar Premium Times, manajan dakin ajiye gawar, Mista Vincent Ude, ya ce yana yin duk mai yiwuwa don gano gawar.
Ya ce:
"Har yanzu ana ci gaba da bincike, na tabbata za mu gano gawar."
Magidanci ya lakadawa budurwa dukan tsiya, ya umarci matarsa ta kashe ta a Kano
A wani labari na daban, wani dattijo dan shekara 50, Ahmadu Muhammad, ya gurfana a gaban kotun shari'ar Musulunci, bisa zargin razana wata mata a jihar Kano.
The Nation ta rahoto cewa, Muhammad, wanda ke zaune a ƙauyen Zaidawa Fulani, karamar hukumar Ɗanbatta, ana tuhumarsa da laifin aikata laifin fin ƙarfi da kuma razanarwa.
Mai gabatar da ƙara daga hukumar yan sanda, Insufekta Abdul Wada, ya shaida wa kotun cewa wata mata mai suna, Hajara Umaru, daga Zaidawa Fulani, ita ce ta shigar da kara a ofishin CID, ranar 20 ga watan Disamba.
Asali: Legit.ng