Jonathan ya ziyarci Buhari a Aso Rock, ya yi masa bayani kan rikicin Mali
- Ana tsaka da rade-radin shirin komawar tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan jam'iyya mai mulki, ya ziyarci Buhari a fadarsa
- Tsohon shugaban kasan Najeriya ya je yi wa Buhari bayani ne kan rikicin mulki na kasar Mali, wanda shi ke jagorantar kwamitin sasanci
- Goodluck Jnathan ya ziyarci Buhari ne a ranar Alhamis bayan halartar taron ECOWAS da yayi ranar Lahadi da ta gabata a kasar Ghana
Aso Villa, Abuja - Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya ziyarci shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadarsa da ke Abuja a ranar Alhamis.
Kamar yadda mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina ya sanar, Jonathan ya yi bayani kan cigaban siyasa da ke faruwa a jamhuriyar Mali.
Adesina ya ce an yi tar na musamman na ECOWAS a kasar Ghana a ranar Lahadi inda aka tattauna kan halin da siyasar kasar Mali ta ke ciki.
Ya ce hakan ne yasa suka samu ganawa tsakanin shugaban kungiyar sasanci na ECOWAS, tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da shugaban kasa Buhari.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A wata takarda ta daban da aka fitar a ranar Alhamis, Buhari wanda ya samu sako daga Kanal Assimi Goita, shugaban mulkin rikon kwarya na Mali, ya dauka alkawarin cewa Najeriya za ta yi duk abinda ya dace ga kasar.
Col. Abdoulaye Maiga, ministan mulki na kasar Mali, wanda ya jagoranci tawagar ya yi bayani ga shugaban kasa Buhari kan taron da suka yi na gyara kasa a Bamako daga ranar 27 ga watan Disamba zuwa 30 ga wata.
Shugaban kasa Buhari da Jonathan sun sa labule a fadar Aso Rock Villa
A wani labari na daban, Mai girma shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya na ganawa da tsohon shugaban kasa, Dr. Goodluck Jonathan.
Rahotanni daga majiyoyi dabam-dabam sun tabbatar da cewa Dr. Goodluck Jonathan ya ziyarci fadar shugaban kasa.
Vanguard tace Jonathan ya ziyarci Aso Rock Villa ne da kimanin karfe 3:00 na yau Alhamis, 30 ga watan Disamba. Har zuwa yanzu ba a samu labarin abin da tsohon shugaban na Najeriya da magajin na sa suka tattauna a kai ba.
Sai dai Dr. Jonathan ya saba ganawa da shugaban kasa inda yake sanar da shi game da aikin da yake yi wa ECOWAS. Tsohon shugaban kasar ne aka zaba domin ya zama jakada na musamman domin sasanta rikicin siyasar kasar Mali.
Asali: Legit.ng