Mai Aski ya daɓa wa dan Acaɓa sukuddireba har lahira kan wata gaddama

Mai Aski ya daɓa wa dan Acaɓa sukuddireba har lahira kan wata gaddama

  • Wata gaddama da ta haɗa wani mai shagon aski da ɗan Acaba a jihar Bayelsa ta yi sanadiyyar mutuwar dayan su
  • Rahoto ya bayyana cewa mai askin ne ya fara tada gaddamar, kafin daga bisani ya fito da makami ya daba wa ɗan acaɓa
  • Kakakin yan sandan jihar Bayelsa yace jami'ai sun kame wanda ake zargi kuma yanzu haka suna kan bincike kan lamarin

Bayelsa - Wani mai shagon Aski, Lucky Diri, ya daba wa wani ɗan Okada, Emeka Christian Udo, sukunddireba har ya mutu kan wata kaddama da ta haɗa su.

Daily Trust ta rahoto cewa yar ƙaramar kaddama ce ta haɗa mutanen biyu a garin Sagbama karamar hukumar Sagbama, jihar Bayelsa.

Mutumin da ake zargin shi ne ya ja wanda aka kashe da gaddama da safiyar Alhamis, kafin daga bisani ya fito da Sukuddireba ya caka masa a hakarkarinsa na hagu.

Kara karanta wannan

Yan ta'addan ISWAP su kai wani mummunan hari mutane na tsaka da Sallah a jihar Yobe

Kisan kai
Mai Aski ya daɓa wa dan Acaɓa sukuddireba har lahira kan wata gaddama Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

A cewar wata majiya daga yankin da lamarin ya faru, an yi gaggawar kai ɗan Acaɓan babban Asibitin domin ceto rayuwarsa amma rai ya yi halinsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rahotanni sun bayyana cewa fusatattun matasan yankin sun ɗauki gawar suka kai ofishin yan sanda, sannan suka dawo shagon mai Askin, amma suka tarar ya tsere.

Wane mataki yan sanda suka ɗauka?

Kakakin yan sanda reshen jihar Bayelsa, SP Asinim Butswat, wanda ya tabbatar da lamarin, yace jami'an tsaro sun kamo Mai Askin, kuma yanzu haka yana tsare.

Yace kwamishinan yan sandan jihar, Ben Nebolisa Okolo, ya bada umarnin gudanar da sahihin bincike kan anihin abin da ya faru.

Kazalika, Kwamishinan ya tabbatar wa mutanen yankin cewa za su miƙa lamarin gaban kotu da zaran an kammala bincike.

Butswat yace:

"Lamarin mara daɗi ya faru ne ranar 6 ga watan Janairu, 2022, a yankin Sagbama. Wanda ake zargin, Lucky Diri, ya shiga hannun yan sanda, kuma yana tsare a sashin binciken manyan laifuka na jiha."

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: Wani mutumi ya yi lalata da mata 10 a Otal da sunan Kwamishinan jiha

A wani labarin kuma Wasu baƙin mutane akalla 600 sun shiga wata jiha a Arewa cikin motoci

Mutane sun shiga tashin hankali yayin da wasu baƙi mutum 600 suka shiga kauyen Maihula dake karamar hukumar Bali ta jihar Taraba.

Wani mazaunin Maihula, Mallam Yakubu Bello, yace mutane sun wayi gari ne kawai sun ga bakin, kuma tuni matasa suka umarci su fice.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262