Ka yi daidai: Shehu Sani ya goyi bayan Buhari kan watsi da batun 'yan sandan jiha, ya fadi dalili
- Ana fargabar cewa samar da ‘yan sandan jihohi zai haifar da illa da matsaloli fiye da alherin da ake tunanin zai haifar
- Wannan shi ne matsayin shugaban kasa Muhammadu Buhari yayin wata hira da aka yi da shi a ranar Laraba, 5 ga watan Janairu
- Shi ma dai tsohon dan majalisar tarayya, Shehu Sani, ya ce wasu gwamnonin za su yi amfani da ‘yan sandan jiha a matsayin makami wajen farmakar 'yan adawarsu
Kaduna - Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya ce yana goyon bayan kin amincewa da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi na samar da ‘yan sandan jihohi a fadin Najeriya.
Kamar dai ra'ayin shugaba Buhari, jigon na jam’iyyar PDP ya ce idan har aka amince da hakan, gwamnonin jihohin da suke kallon kansu a matsayin alloli za su yi amfani da jami'an ta hanyar da bata dace ba.
Sani ta shafinsa na Facebook a ranar Laraba, 5 ga watan Janairu, ya kai ga zargin cewa wasu gwamnonin za su tabbatar da cewa an dauki ‘yan daban siyasa a cikin rundunar domin cimma manufarsu kan 'yan adawarsu.
Ya ce rundunar ‘yan sandan jiha za ta zama sak, tamkar hukumar zabe mai zaman kanta ta jiha (SIECOM).
A kalamansa:
"Ina goyon bayan Shugaba Buhari wajen adawa da samar da 'yan sandan Jihohi. Idan ka bar wasu gwamnonin jihohi suka mallaki 'yan sanda na kansu, za su dauki 'yan daba da magoya bayansu na siyasa cikin irin wadannan 'yan sanda… kuma za su tsananta wa abokan adawar siyasa da masu sukarsu ba wai 'yan bindiga ko 'yan ta'adda ba. Za su tafiyar da jami'an kamar SIECOM."
Buhari ya yanke hukunci na karshe kan batun samar da 'yan sandan jihohi
Tun farko, a karo na biyu, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ki amincewa da samar da ‘yan sandan yankuna, The Nation ta ruwaito.
Ya yarda da cewa jihohi da dama ba za su iya daukar nauyinsu ba kuma yana tsoron a yi amfani da su ta wata hanyar da bata dace ba.
‘Yan Najeriya da dama sun nuna bukatar samar da ‘yan sandan ciki har da gwamnonin jihohi don kawo karshen rashin tsaro da ya yi wa kasar nan katutu.
Asali: Legit.ng