Dubu ta cika: Wasu masu tone kabari su sace sassan jikin mamata sun shiga hannu

Dubu ta cika: Wasu masu tone kabari su sace sassan jikin mamata sun shiga hannu

  • Wasu mutane da ke tone makabarta su sace gawarwaki sun shiga hannu yayin da suke aikata mummunan aikin
  • An kama su da kawunan mutane 16 da sauran sassan jikin mamata da aka binne a wata makabarta a Kudu
  • Lamarin dai an jima ana zargin faruwarsa, kuma tuni aka mika su ga 'yan sanda domin ci gaba da bincike kan lamarin

Oyo - A jiya Laraba ne aka kama wasu mutum biyu masu matsakaicin shekaru a yayin da suke tono kawuna 16 da sassan jikin mamata daga wata makabarta a hanyar Moniya-Iseyin, Iseyin ranar Talata.

Wadanda ake zargin dai su ne Alfa Yunusa Atikoko, da Wasiu Ajikanle.

Daily Trust ta tattaro cewa mutanen Odua People’s Congress (OPC) da Yoruba Revolutionary Movement (YOREM) ne suka kama su a unguwar Alamole.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun kama wasu mutane 2 da suka kashe malamin addini suka sace kuɗinsa bayan ya basu masauki

Mabarnata sun tone kabari a Oyo
Dubu ta cika: Wasu masu tone kabari su sace sassan jikin mamata sun shiga hannu | Hoto: channelstv.com
Asali: Twitter

An kama su ne bayan sun tono gawarwakin tare da ajiye abubuwan da suka cire a cikin buhuna.

Wani ganau ya shaida cewa an mika wadanda ake zargin ga ‘yan sanda domin ci gaba da bincike da kuma gurfanar da su a gaban kuliya.

Majiya ta ruwaito cewa an samu korafe-korafe game da bacewar gawarwakin da aka binne a makabartar da hukumomi a makabartar suka kasa tantancewa.

Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, Adewale Osifeso, ya ce nan ba da dadewa ba za a samar da bayanan da suka dace a nan gaba.

Ba wannan ne karon farko da ake samun irin wannan barna ba. A watan Satumban 2022, an sami irin wannan aiki a Kaduna, kamar yadda Vanguard ta tattaro.

Kara karanta wannan

Maimakon mika wa 'yan sanda, 'yan banga sun hallaka 'yan leken asirin 'yan bindiga a Zamfara

'Yan bindiga sun tafka barna a Zariya, sun kashe mutane sun saci dabbobi

A wani labarin, wasu ‘yan bindiga sun kashe mutane tara tare da raunata wasu biyar da kuma sace dabbobi sama da 250 a hare-haren da suka kai a karamar hukumar Igabi da Zaria a jihar Kaduna.

An tattaro cewa 'yan bindigan sun fara kai hari ne a unguwar Kudu da Gari dake Sabon Birni a karamar hukumar Igabi inda suka kashe mutane bakwai tare da jikkata wasu hudu, Daily Trust ta rahoto.

A wani matsugunin makiyaya kuwa mai suna Ruggar Goshe da ke wajen kauyen Kangimin Sarki a Rigachikun a karamar hukumar Igabi, ‘yan bindigar sun harbe Auwal Koshe har lahira tare da sace awaki da tumaki kusan 250.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.