'Dan Sanda Abokin Kowa: Lokuta 4 da ƴan sandan Najeriya suka yi wa mutanen da basu sani ba manyan abin alheri

'Dan Sanda Abokin Kowa: Lokuta 4 da ƴan sandan Najeriya suka yi wa mutanen da basu sani ba manyan abin alheri

Kamar ko wanne aiki a duniyar nan, akwai mutane iri biyu, masu kirki da akasin hakan.

Sai dai ga ko wanne aiki, akwai abubuwa munana da wasu su ke yi wanda su ke janyo bacin suna ga ‘yan uwan aikinsu a idon duniya, kamar yadda wasu bata gari su ka shafa wa rundunar ‘yan sandan Najeriya kashin shanu.

'Dan Sanda Abokin Kowa: Lokuta 4 da ƴan sandan Najeriya suka yi wa mutanen da basu sani ba abin alheri
Lokuta 4 da 'yan sandan Najeriya suka yi wa mutanen da ba su sani ba gagarumar alheri. Photo Credit: Celestina Nwankwo, LinkedIn/Joel Nwokeoma
Asali: Facebook

Sai dai akwai wasu zakakuran ‘yan sanda wadanda su ka taimaka wa ‘yan Najeriyan da basu sani ba wanda hakan ya dawo da sunan rundunar kuma ya shayar da jama’a da dama mamaki.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Buhari ya yanke hukunci na ƙarshe kan batun samar da 'yan sandan jihohi

Legit.ng ta hasko wasu jami’ai 4 na ‘yan sanda wadanda su ka sadaukar da rayuwarsu da dukiyoyinsu wurin nuna wa wasu kauna da taimako na musamman.

1. Jami’ar ‘yan sandan da ta biya wa wasu dalibai kudin makaranta

Faith Okwuego Ejoh, ita ce ‘yar sandan da ta dauki hankalin mutane a kafafen sada zumunta bayan an samu labarin ta biya wa dalibai 19 kudin makaranta daga jihar Delta.

Bayan samun labarin aikin alherin nata, wani dan jarida wanda ya yada labarin a kafafen sada zumunta ya kambama ta tare da cewa:

“Mutuniyar kirki ce mai zuciyar gwal. Ku taya ni yaba wa wannan baiwar Allar akan wannan kokari da ta yi. Tabbas haske daga wurin ka yana gusar da duhun na kusa da kai.”

2. Jami’ar ‘yan sandan da ta ceci rayuwar wani matashi bayan barayi sun harbe shi

Wani dan Najeriya, Ajabor Friday, ya kara samun damar rayuwa bayan wata ‘yar sanda, CSP Celestina Nwankwo Kalu ta ceci rayuwarsa.

Kara karanta wannan

Garkuwa da mutane: Dakarun ‘Yan Sanda sun kubutar da mutum kusan 100 daga jejin Zamfara

Legit.ng ta ruwaito yadda barayi suka harbi wani matashi inda suka barsa kwance rai a hannun Allah.

Wata ‘yar sanda ta yi gaggawar cetonsa kuma ta tabbatar ya samu duk wata kulawar da ta dace inda ta kashe N400,000 duk da bata da wata alaka da shi.

3. Dan sandan da ya ba direban Napep da fasinjoji kudi don siyayyar kirsimeti

Ranar jajibarin kirsimeti, an samu wani bidiyo wanda ya yadu a kafafen sada zumunta wanda aka ga jami’in yana ba direba da sauran fasinjojin Napep kyautar kudade.

Da farko dan sandan ya fara tsayar da direban ne tare da duba takardun Napep din kafin ya ba direban da sauran fasinjoji kyautar ta musamman.

Daga direban har fasinjojin sun cika da mamaki wanda hakan ya sa su ka kasa magana.

4. Dan sandan da ya raba wa mata da direban Napep shinkafa

Wani dan sanda wanda ba a gano sunansa ba ya ba fasinjoji da direban Napep kyautar shinkafa washegarin kirsimeti.

Kara karanta wannan

Jami’an tsaro sun damke matar auren da ta ke kai wa ‘Yan bindiga yaranta domin su yi lalata

A bidiyon wanda shafin @instablog9ja ya wallafa an ga yadda ya fara da gaisawa da direban da kuma matan cikin Napep din kafin ya ciro buhun shinkafan daga bayan motarsa sannan ya ba su kyauta.

Nan da nan su ka dinga yi masa addu’o’i na fatan alheri da godiya mara adadi.

Shugaban wurin aiki ya ba na ƙasa da shi da ke tattaki zuwa wurin aiki kyautar mota

A baya, kun ji wani matashi, Walter, ya yi tattakain mil 20 a ranar sa ta farko ta zuwa wurin aiki. Motar sa ta samu matsala ana gobe zai fara zuwa aikin hakan ya sa ya yanke wannan shawarar.

Kafin safiyar, ya yi kokarin tuntubar abokan sa amma babu alamar zai samu tallafi saboda ya sanar da su a kurarren lokaci kamar yadda Understanding Compassion ta ruwaito.

Daga nan ne ya yanke shawarar fara tattaki tun karfe 12am don isa wurin aikin da wuri. Matashin bai bari rashin abin hawan ya dakatar da shi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164