Bayan cikar watanni uku, Gwamna El-Rufa'i ya kara wa'adin hana Acaba a jihar Kaduna

Bayan cikar watanni uku, Gwamna El-Rufa'i ya kara wa'adin hana Acaba a jihar Kaduna

  • Gwamnatin Kaduna ta kara wa'adin hana Okada, yawo da makami da sauran matakan da ta ɗauka har sai baba ta gani
  • Kwamishinan tsaro da al'amuran cikin gida, Samuel Aruwan, yace matakan na nan daram har sai gwamnati ta fitar da sanarwa
  • Gwamnatin ta kuma kara baiwa al'umma hakuri tare da bukatar su cigaba da biyayya ga dokokin domin samun tsaro a jihar

Kaduna - Gwamnatin jihar Kaduna ta kara wa'adin hana amfani da mashin, wanda aka fi sani da 'Okada' ga yan kasuwa da kuma ɗai-ɗaikun mutane har sai baba ta gani.

Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da kwamishinan tsaro da harkokin cikin Gida, Samuel Aruwan, ya fitar a shafinsa na Facebook ranar Talata.

Gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai
Bayan cikar watanni uku, Gwamna El-Rufa'i ya kara wa'adin hana Acaba a jihar Kaduna Hoto: Nasir El-Rufai
Asali: Facebook

Kwamishinan yace hana Okada da sauran matakan da gwamnatin jihar Kaduna ta ɗauka na nan daram.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Yan bindiga sun sun yi awon gaba da matan aure da yan mata a sabon harin jihar Kaduna

Aruwan yace:

"Gwamnatin Kaduna na sanar da al'umma cewa hana amfani da mashin, wato Okada, yana nan daram har sai baba ta gani."

Wane matakai ne Gwamnatin Kaduna ba ta dage ba?

Sauran matakan da gwamnatin jihar ta ɗauka, wanda a cewar Aruwan za su cigaba da kasancewa har sai an ji daga gwamnati, sune kamar haka:

1. Hana yawo da makamai masu hatsari.

2. Hana amfani da mashin mai kafa uku wanda aka fi sani da Keke Napep da daddare, (Wato daga karfe 7:00 zuwa karfe 6:00 na safe) a kananan hukumomin Birnin Gwari, Giwa, Igabi, Chikun, Kachia, Kagarko da kuma Kajuru.

Mutane su cigaba da hakuri

Gwamnatin jihar Kaduna na cigaba da jajantawa al'umma bida halin matsi da waɗan nan matakan ka iya jefa su, a cewar kwamishinan.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ta san abun yi don kawo karshen rashin tsaro cikin watanni 17 – Gwamnan APC

Ya kuma kara da kira ga dukkan mazauna jihar Kaduna da su yi biyayya ga waɗan nan matakan domin tsaron mutane baki ɗaya.

A wani labarin kuma Sheikh Ahmad Gumi ya maida zazzafan martani kan kashe shugabannin yan bindiga a Zamfara

Yayin da yan Najeriya ke murnan nasarar da sojiji suka samu a Zamfara na kashe shugabannin yan binidga, sansanin shahararren malamin nan, Sheikh Gumi, ya nuna tantama kan lamarin.

Bangaren Malamin, waɗan da ke ganin hanyar sulhu ce kaɗai mafita, ya yi kira ga rundunar soji ta tabbatar da ikirarinta ta hanyar bayyana hujjoji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262