Kwankwaso: Babu shakka an yi wa Ganduje warwas a zaben 2019, masu iko suka makala wa Kano
- Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, tsohon gwamnan jihar Kano, ya bayyana cewa ko shakka babu an yi wa Gwamna Ganduje warwas a zaben 2019
- Kwankwaso ya ce wasu masu karfin iko ne suka lakaba wa jihar Kano Ganduje, abinda ya misalta da mafi munin laifin da aka yi wa damokaradiyya
- Jigon Kwankwasiyyar yace, a yanzu haka ana fuskantar illa wannan take hakkin talakawa da aka yi inda aka danne hakkinsu duk da sune masu rinjaye
Kano - Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwannkwaso, ya ce gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya fadi zaben 2019 amma wasu masu iko ne suka makalawa jihar.
A wata tattaunawa da The PUNCH, Kwankwaso ya kwatanta zargin lakabawa Kano Ganduje da "mafi munin laifin da aka yi a damokaradiyya".
Tsohon gwamnan ya ce da yawansu sun gane kuskurensu kuma sun shirya canzawa a jihar nan da 2023.
"Kasar nan ta san cewa Ganduje ya fadi zaben 2019 a Kano, amma masu iko ne suka tabbatar da sun manna wa masu rinjayen," yace.
Ya kara da cewa:
"Abinda marasa rinjaye ke so aka mannawa masu rinjaye wanda ya zama shi ne mafi munin laifin damokaradiyya. Ina tunanin kowa na fuskantar sakamakon hakan. Ina tunanin wasu suna kokarin gane kuskurensu bayan tsananin barnar da aka yi wa jihar.
"Abun takaici ne yadda mutane basu ganin abinda talakawa ke gani. Akwai dalilan da suka sa da ba a bar shi ya yi takara ba a 2019, amma masu iko suka nace cewa sai ya cigaba.
"Talakawa sai suka yi abinda shugabannin suka kasa yi. Daga nan sai suka sake amfani da ikonsu a kan mutane. Sai kuma wadanda ba su son fara tashin hankali a jihar suka hakura."
Tsohon ministan ya ce akwai matasa masu tarin yawa da ke shiga jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) kafin zuwa zaben 2023, TheCable ta ruwaito.
A sakon sabuwar shekara, Ganduje ya yi magana kan sasanci da Kwankwaso da tsagin Shekarau
A wani labari na daban, Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya magantu kan bukatarsa na sasantawa da abokin hamayyarsa, tsohon Gwamna Rabiu Kwankwaso da tsagin APC karkashin shugabancin Sanata Ibrahim Shekarau.
A sakon sabuwar shekara, wanda kwamishinan yada labarai na jihar, Muhammad Garba yasa hannu a ranar Juma'a, Ganduje ya ce zai sadaukar da sabuwar shekarar wurin tabbatar da sabon tsarin zaman lafiya da sasanci tsakanin masu ruwa da tsakin jam'iyyun siyasa a jihar da kasar baki daya, Daily Nigerian ta ruwaito.
Daily Nigerian ta ruwaito cewa, duk da gwamnan bai kira sunayen 'yan siyasan ba, takardar ta jaddada bukatar shugabannin kungiyoyin siyasa na jihar da su hada kai domin kawo sabon tsari a siyasar jihar.
Asali: Legit.ng