Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun yi awon gaba da tsohon dan takarar gwamna a jihar Arewa
- Yan bindiga sun kutsa har cikin gidan wani jigon PDP a jihar Filato dake arewa ta tsakiya, sun yi awon gaba da shi
- Wani abokinsa ya tabbatar da cewa maharan sun kira wayar ɗaya daga cikin yayansa, sun nemi a haɗo musu miliyoyi kudin fansa
- Rahoto ya nuna cewa maharan sun sace tsohon ɗan takarar gwamna karkashin PDP ranar 1 ga watan Janairu, 2021
Plateau - Wasu yan bindiga sun yi awon gaba da tsohon ɗan takarar gwamnan jihar Filato a zaben 2019 da ya gabata, Nkemi Nicholas Nshe.
Punch ta rahoto cewa Nshe, babban jigon jam'iyyar PDP a jihar Filato, ya shiga hannun yan bindiga ne a gidansa dake yankin karamar hukumar Shendam.
Tsohon dan takarar gwamnan ya yi aiki a matsayin ciyaman din karamar hukumarsa ta Shendam a lokuta daban-daban da suka gabata.
Bugu da kari, shi kansa gwamna mai ci, Simon Lalong, ya fito ne daga yankin Shendam dake kudancin jihar Filato.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Majiyoyi da dama sun tabbatar mana da rahoton sace Nshe a gidansa ranar Lahadi da safe.
Yadda lamarin ya faru
Wani abokin Nshe a Shendam, wanda ya koka da sace tsohon ciyaman ɗin su, ya shaida mana cewa lamarin ya fara tada hankulan mutane a yankin.
Vanguard ta rahoto Mutumin yace:
"Ku tama mu addu'an fatan kubutar Dakta Nkemi Nshe, wanda mahara suka tilasta masa bin umarninsu suka tafi dashi daga gidansa a Shendam da safiyar Asabar, wacce ta kasance sabuwar shekara, 1 ga watan Janairu, 2022."
"Yan bindigan sun kutsa gidansa da daddare, suka yi awon gaba da shi, amma ba su tafi da wayarsa ba, lamarin dai babu dadi."
Shin sun nemi kudin fansa?
Ya ƙara da cewa ya samu labarin maharan sun tuntubi iyalan Dakta Nshe a cikin yinin ranar Asabar, kuma sun nemi a biya kudin fansa.
"Amma jiya da yammaci (ranar Asabar) na samu labarin yan bindigan sun tuntubi iyalansa ta lambar wayar ɗansa, sun nemi a tattara musu miliyan N100m kudin fansa amma daga baya sun sakko zuwa miliyan N50m."
"Ina za su samu wannan kudin a lokacin da mutane ke shan wahala? Abin yana bani mamaki yadda FG ta tilasta wa kowa ya yi rijistan layin waya amma irin haka na faruwa ba tare da kame yan ta'addan ba."
Wane mataki yan sanda suka ɗauka?
Da aka tuntubi kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Filato, Ubah Ogaba, ya ce zai binciko cikakken bayani kan lamarin sannan ya dawo gaare mu.
A wani labarin na daban kuma Gwarazan yan sanda sun damke kasurgumin dan binidga da ya addabi Zamfara, kuma sun ceto mutane da dama
Rundunar yan sanda reshen jihar Zamfara ta bayyana cewa jami'anta sun samu nasarar kame wani kasurgumin dan bingida, Sani Mai Yan Mata, wanda ya addabi yankin Zurmi-Shinkafi.
Kwamishinan yan sandan jihar, CP Ayuba Elkana, ya sanar da cewa ɗan bindigan na kan hanyar kai hari kan matafiya, yayin da jami'ai suk rutsa shi, kuma suka kama shi.
Asali: Legit.ng