Ba yaƙi na ke yi da Buhari ba, Sunday Igboho ya fitar da saƙon sabuwar shekara
- Mai neman kafa kasar Yarbawa, Cif Sunday Adeyemo wanda aka fi sani da Sunday Igboho, ya ce ba fada ya ke yi ba da Shugaba Muhammadu Buhari
- Sai dai ya ce yana bakin cikin ganin yadda gwamnatin Buhari ta ke sakaci ne da batun tsaro musamman a yankunan al'ummar Yarbawa a kasar
- A sakonsa na sabon shiga sabon shekarar 2022, Igboho ya ce kowa da ke zaune a kasar yana da hakkin a bashi kariya a kuma tsare masa mutuncinsa
Mai rajin kare hakkin Yarbawa, Sunday Adeyemo da aka fi sani da Sunday Igboho, a ranar Juma'a cikin sakon sa na sabuwar shekara ya ce ya yaƙi ya ke yi da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ba ko wani a gwamnatin, rahoton The Punch.
Sunday Igboho cikin sakon nasa mai dauke da sa hannun ɗaya daga cikin lauyoyinsa a Najeriya, Pelumi Olajengbesi, ya ce rashin tsaro a kudu maso yamma ne yasa ya fara fafutikan ɓale wa daga kasar.
Ba fada na ke yi da Buhari ba ko gwamnoni, tsaro na ke son a bawa mutane na, Igboho
Sanarwar ta taken 'Sakon sabon shekarar 2022 na Sunday Igboho' ta ce; Muna son mu fayyace cewa bana yaƙi da Shugaba Buhari, Gwamnoni ko wani a gwamnati.
"Abin da na ke so shine gwamnati ta magance ainihin dalilin da yasa na fara fafutikan neman kafa kasar Yarbawa.
"Ainihin matsalar shine rashin tsaro a Ibarapa da sauran yankunan Yarbawa inda ake kai wa manoma hari ana kashe su, ana sace su tare da yi wa mata fyade kamar ba jami'an tsaro a kasar. Kowa na da hakkin a bashi tsaro ba tare da la'akari da kabila, addini ko siyasa ba
"A wani lokaci, mutanen mu sun shiga mawuyacin hali har sun kasa zuwa gona. An kashe manoma da dama a 2021 kuma gwamnati ta saki jiki kamar hakan ba komai bane. A'a, ba za mu cigaba haka ba shi yasa na tashi don dakile matsalar. Ba na yi magana bane don fada da gwamnati, na yi magana ne don tabbatar an bawa mutanen mu tsaro.
"Sako na a 2022 shine gwamnati ta tashi tsaye ta kawo karshen hare-haren makiyaya da bata gari don kowa ya samu natsuwa - ƴan Najeriya ko ƴan kasar waje - a dena kai mana hari a kasar Yarbawa.
"Ni ba mutum mai son kai bane, na fi damuwa ne da mutanen da suka birne yan uwansu a 2021 kuma ina addu'a Allah ya kawo karshen kashe-kashen ƴan Najeriya da ba su ji ba ba su gani ba."
Tunda farko, Legit.ng ta rahoto cewa an kama Igboho an tsare shi a gidan yari a Cotonou, Jamhuriyar Benin, yayin da ya ke hanyar tserewa zuwa Jamus.
Ya shafe kimanin kwana 161 a tsare a gidan yarin kuma ba a san ranar sakinsa ba.
Buhari: Bisi Akande Mai Gaskiya Ne, Bai Taɓa Amsa Ko Bayar Da Cin Hanci Ba
A wani labarin, Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana Cif Bisi Akande, tsohon shugaban riko na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a matsayin ma'aikacin gwamnati mai gaskiya da rikon amana, Daily Trust ta ruwaito.
Buhari, wanda shine babban bako na musamman wurin gabatar da littafi da Bisi Akande ya rubuta kan rayuwarsa ya ce marubucin bai taba sauya halinsa ba tun yana aikin gwamnati da bayan ya gama, na rashin karba ko bada rashawa.
Ya karanto daga shafi na 400 a cikin littafin inda Akande ya rubuta cewa bai taba nema ko bada cin hanci ba a rayuwarsa, ya kuma jadada cewa kamilin mutum ne mai gaskiya.
Asali: Legit.ng