Bidiyon dan achaba dauke da fasinjoji 7 reras ya janyo cece-kuce
- Wani dan acaba ya ba mutane da dama mamaki a yanar gizo bayan bayyanar wani bidiyon babur dinsa wanda ya bambanta da sauran babura
- Babur din ya na da mazauni mai tsawo wanda mutane 7 za su iya jeruwa a kai kuma su zauna ba tare da sun takura ba har a yi tafiya
- Mutane da dama sun dinga caccakar babur din na daban inda su ke cewa zai iya zama hatsari ga mai tukin da kuma masu hawa
Wani dalili na iya janyo wa mutum ya kirkiro abinda ba a taba gani ba, amma wannan kirkirar babur din na musamman ya shayar da mutane da dama tsananin mamaki.
A wani bidiyo wanda ya yadu a kafafen sada zumuntar zamani, an ga yadda wani mutum ya ke tuka wani babur mai doguwar kujera.
Shafin goldmynetv ya wallafa bidiyon a Instagram, kuma an ga wani babur da zai iya daukar mutane 8 inda daya zai kasance mai tuki yayin da sauran wurin zai isa fasinjoji 7 duk a lokaci guda.
Bidiyon ya dauki hakalin mutane da dama bisa yadda aka ga mata da maza su na hawa babur din ba tare da nuna damuwarsu ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Yayin da mai tukin babur din ya ajiye kafafunsa a kasa, nan da nan fasinjoji su ka dinga hawa har sai da su ka kai 7.
Daga nan ya ja babur din a sannu a hankali. Legit.ng ba ta gano inda aka dauki bidiyon babur din ba har lokacin rubuta rahoton.
Jama'a sun yi martani
Nan da nan mutane su ka hau cece-kuce a kafafen sada zumunta.
@officalg9ice ya ce:
“Sai na tsayar da wannan babur din in har da na gan shi a hanyar duk da ni ba dan sanda bane... Kai!!”
@abilitywithoutvalidity ya ce:
“Mummunan abinda zai faru shi ne idan su ka zube a kasa yadda makaman da ke hannunsu za su cutar da su. Ubangiji ya kare su.”
@wonders53 ya ce:
“Babu abinda ba za ka gani ba a kasashen nahiyar Afirka da ke yaren Faransa, shirmensu ya yi yawa. Ya direban ya ke ganin hanya?”
@simisidtours ta ce:
“Nan Douala ne a kasar Kamaru. Yadda ake amfani da babur abin tsoro ne.”
Hotunan tsoho mai shekaru 88 ya kammala digiri rana daya da jikarsa mai shekaru 23
A wani labari na daban, ba a san maci tuwo ba sai miya ta kare. Wani tsoho mai shekaru 88 ya tabbatar da wannan karin maganar bayan cika burinsa wanda ya dauki tsawon lokaci a zuciyarsa.
Yan Bindiga Sun Sake Tare Motocci a Hanyar Kaduna-Birnin Gwari, Sun Bindige Mutane 6, Sun Sace Da Dama
Ya samu nasarar kammala digirinsa a jami’ar Texas da ke San Antonio inda ya yi karatu a fannin tattali.
Abinda zai kara burge mai karatu akan labarinsa shi ne yadda ya kammala digirin tare da jikarsa, Melanie Salazar.
Asali: Legit.ng