Rundunar 'yan sanda ta kame jami'in dan sandan da aka ga yana karbar cin hanci a wani bidiyo

Rundunar 'yan sanda ta kame jami'in dan sandan da aka ga yana karbar cin hanci a wani bidiyo

  • Hukumar 'yan sandan Abuja ta kama wani jami'inta da aka ga yana karbar cin hanci a wani bidiyo
  • Tuni rundunar ta kaddamar da bincike a cikin al'amarin kamar yadda mai magana da yawun 'yan sandan birnin tarayya, Josephine Adeh ta bayyana
  • Rundunar ta kuma saki wasu lambobin waya da jama'a za su dunga shigar da kara kan abubuwa makamancin haka

Abuja - Rundunar 'yan sandan birnin tarayya ta kama wani jami'in dan sandan da aka ga yana karbar cin hanci a wani bidiyo da ya shahara a shafin Instagram, rahoton Nigerian Tribune.

Mai magana da yawun 'yan sandan birnin tarayya, Josephine Adeh wacce ta sanar da hakan ta bayyana cewa CP Babaji Sunday ya kafa kwamitin bincike kan lamarin, The Guardian ta rahoto.

Kara karanta wannan

An kama wasu da suka bi dare suka sace shanu 2 a gidan wani a Jigawa

Rundunar 'yan sanda ta kame jami'in dan sandan da aka ga yana karbar cin hanci a wani bidiyo
Rundunar 'yan sanda ta kame jami'in dan sandan da aka ga yana karbar cin hanci a wani bidiyo Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Adeh ta ce:

"An ja hankalin rundunar 'yan sandan birnin tarayya zuwa ga wani wallafa da yayi fice na zargin cin hanci da wasu jami'an 'yan sanda ke yi a Abuja.
“Sakamakon haka, Kwamishinan ‘yan sandan babban birnin tarayya, CP Sunday Babaji, ya bayar da umarnin gudanar da bincike cikin gaggawa tare da cafke jami’an da ke da hannu a cikin wannan aika-aika.
“Saboda haka an fara bincike kuma sakamakon zai bayyana a fili bayan kammalawarsa.
“Yayin da yake tabbatar wa da jama’a cewa za su gudanar da bincike mai zurfi, CP ya bukaci mutanen babban birnin tarayya Abuja da su dunga tuntubar Hukumar Korafe-korafen Jama’a a lamba 09022222352, layin da aka sadaukar domin karba da kuma sauraron korafe-korafen rashin da'a da jami’an rundunar suka yi.

Kara karanta wannan

Karya ne yan bindiga basu kai hari mahaifar sakataren Buhari a Adamawa ba – Yan sanda

"Rundunar ta kuma bukaci mazauna yankin da su bayar da rahoton duk wani motsi da basu aminta da shi ba ta wadannan layukan: 08032003913, 08061581938, 07057337653 da 08028940883."

A wani labari na daban, mun ji cewa mazauna garin Dansadau da ke jihar Zamfara sun yi bikin wata daya ba tare da harin yan bindiga ba. Audu Bulama Bukarti, wani mai rajjin kare dan Adam ne ya bayyana hakan.

A cewarsa, wannan bikin bai kasance sakamakon kokarin gwamnati ba. Ya ce yan bindigar basu kai wa mutanen hari ba saboda sun kulla yarjejeniya da su.

Ya ce:

“A yau, mutanen Dansadau na Zamfara sun yi bikin cika wata daya ba tare da hari ba. Amma kafin Ku fara jinjinawa da zagin manyan masu fada aji...Wannan bai kasance sakamakon kokarin gwamnati ba. Ya kasance ne saboda mutanen Dansadau sun kulla yarjejeniya da yan ta’addan. Sun ce sun mika wuya ga yan ta’addan saboda gwamnati ta gaza masu. Shin akwai gazawar da ta fi ta gwamnati? Menene aikin gwamnati?”

Kara karanta wannan

Bakon lamari: Bidiyon dan sanda na raba wa matafiya buhunan shinkafa ya jawo cece-kuce

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng