TRCN ta magantu kan shirin Buhari na fara biyan daliban digiri da NCE kudin kashewa

TRCN ta magantu kan shirin Buhari na fara biyan daliban digiri da NCE kudin kashewa

  • Hukumar rijistar malamai ta Najeriya (TRCN) ta yi karin haske kan shirin gwamnatin tarayya na fara baiwa daliban ilimi alawus alawus a duk zangon karatu
  • Farfesa Josiah Ajiboye, magatakardan TRCN, ya ce za a sanar da jama’a cikakkun bayanai kan batun alawus din na kowane zango a watan Janairun 2022
  • A wani yunkuri na samar da kwararrun malamai, gwamnatin tarayya ta yi alkawarin bullo da alawus ga daliban fannin ilimi a jami’o’in gwamnati da sauran manyan makarantu

Abuja - Kungiyar yiwa malamai rijista a Najeriya ta TRCN ta ce cikakken bayani kan alkawarin alawus na zangon karatu (N75,000) da shugaban Buhari ya yi wa daliban fannin ilimi a jami'o'in gwamnatin tarayya da kwalejojin ilimi na tarayya zai fito nan da wata mai zuwa.

TRCN ta bayyana cewa tuni aka rubuta wasiku kuma ma’aikatar ilimi tana aiki tare da Asusun Tallafawa Manyan Makarantu a kan haka.

Kara karanta wannan

Mummunar gobara ta yi kaca-kaca da wasu kasuwanni biyu a jihar Sokoto, ta kone shaguna

Batun fara ba da alawus na daliban jami'a da FCE
Ilimi: Saura kiris maganar fara ba daliban jami'a tallafin N75k a duk zango ya tabbata | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Facebook

Magatakardar hukumar ta TRCN, Farfesa Josiah Ajiboye ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa ta wayar tarho da wakilin jaridar Punch a ranar Laraba.

A baya an Tribune da sauran kafafen yada labarai sun ruwaito cewa Buhari a lokacin bikin ranar malamai ta duniya na shekarar 2021 ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta sa harkar koyarwa ta yi daraja sosai tare da tabbatar da cewa malamai sun samu isasshen horo.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kuma bayyana cewa daliban fannin ilimi a cibiyoyin gwamnati za su samu alawus na kowane zango na N50,000 ga wadanda ke kwalejojin ilimi da kuma N75,000 ga wadanda ke jami’o’i.

Shugaban na TRCN a baya ya shaida cewa gwamnatin tarayya ta kafa wani kwamiti da ya kunshi wakilan majalisar kasa da hukumar albashi da kudaden shiga da shugaban ma’aikatan tarayya da ma’aikatar ilimi.

Kara karanta wannan

Kwastam ta yi babban kamu, ta kame kwantena makare da tramadol na biliyoyi

Amma a ranar Laraba, ya ce cikakken bayani game da aiwatar da aikin zai bayyana a watan Janairun 2022.

A cewar Ajiboye:

“Ministocin da abin ya shafa sun shirya wasiku kuma suna aiki tare da TETFUnd. An yi dukkan abubuwan da suka dace; za a bayyana bayanai a watan Janairu."

Gwamnatin Buhari za ta fara biyan daliban digiri da NCE kudin kashewa

A tun farko, gwamnatin Tarayya ta amince da biyan N75,000 a matsayin alawus-alawus na kowane zango ga daliban da ke karatun digiri a fannin Ilimi a jami'o'in gwamnati a Najeriya, Punch ta ruwaito.

Hakanan, daliban NCE za su karbi N50,000 a matsayin alawus na kowane zango a wani kokarin gwamnati don jawo hankalin samar da kwararrun malaman makaranta kamar yadda Shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya) ya yi alkawari shekaran da ya gabata.

Ministan Ilimi, Adamu Adamu, ya sanar da hakan a ranar Talata 5 ga watan Oktoba, a bikin ranar malamai ta duniya da aka gudanar a Eagle Square da ke babban birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Sojojin Najeriya sun yi babban kamu, sun cafke wani kasurgumin shugaban IPOB

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.