An damke wani matashin dan bindiga yana kokarin tare hanya, an kwato mutum 10 daga hannunsa
- Dan bindiga mai shekaru 20 da haihuwa ya shiga hannun yan sanda yayinda yake kokarin awon gaba da matafiya
- Kwamishanan yan sandan jihar tare da jami'ansa sun gurfanar da matashin gaban yan jarida
- An samu nasarar ceto mutane goma daga hannunsa cikin wadanda aka sace ranar Talata a jihar
Zamfara - Jami'an hukumar yan sanda a jihar Zamfara sun samu nasarar damke kasurgumin dan bindiga wanda ya addabi kananan hukumomi uku a Arewacin jihar.
Dan bindiga, wanda dan shekara 20 ne kacal ya kasance yaron gidan Bello Turji amma ya koma karkashin wani shahrarren dan bindiga Kachalla Sani Black.
TVCNews ta ruwaito cewa an damke wannan matashi ne yayinda yake kokarin tare matafiya a hanyar garin Kaliya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Jami'an yan sandan sun bayyana cewa an damkeshi da bindiga AK47, carbin harsasai uku da Babur kirar Boxer.
An ceto mutum goma da ya sace a kauyen Gada dake karamar hukumar Bungudu. Daga cikinsu akwai Mai raino da jaririnta.
An sace su ne lokacin da yan bindigan suka dira garin ranar Talata inda aka kai hari gidan Hakimin gari, Alhaji Umaru kuma suka kasheshi.
Abin da ya sa matsalar tsaro ke neman gagarar hukuma - Hamza Al-Mustapha ya fadi sirrin
A bangare guda, Manjo Hamza Al- Mustapha wanda ya taba zama jami’in da ke kula da tsaron Janar Sani Abacha, ya yi magana game da sha’anin rashin tsaro a Duniya.
Jaridar Vanguard ta rahoto Manjo Hamza Al- Mustapha yana zargin masu kudi da hannu a matsalar tsaron da ya addabi jihohi da dama yanzu a Najeriya.
Hamza Al-Mustapha yace attajiran da su ke iya mallakar manyan makamai da miyagun kwayoyi ne ummul-haba’isin halin da al’umma suka shiga ciki a yau.
Da yake zantawa da manema labarai a gidan rediyon VOA, Manjo Al- Mustapha ya bayyana cewa akwai bukatar masu kishin kasa su hada-kai, su ceto Najeriya.
Asali: Legit.ng