Yadda aka kama ni, mahaifina da yan uwana da zargin kisa, Gwamna

Yadda aka kama ni, mahaifina da yan uwana da zargin kisa, Gwamna

  • Gwamna Wike na jihar Ribas ya bayyana cewa ba zai taɓa mantawa da halaccin lauya Ukala SAN ba a rayuwarsa
  • Wike yace akwai lokacin da aka kama shi, mafaifinsa da sauran yan gidansu maza da zargin kisa, amma Ukala ya tsaya musu
  • Yace ko bayan zaben 2015 lokacin da kotu ta soke zaben jihar Ribas, Ukala ne ya tsaya masa har ya samu nasara

Rivers - Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya bada labarin yadda rikicin mukami a kauyensu ya yi sanadin kama shi, mahaifinsa da sauran iyalan gidan su.

Wike ya faɗi haka ne yayin da yake yaba wa babban lauya Emmanuel C. Ukala, (SAN) a wurin taron bikin cikarsa shekara 65, kamar yadda daily trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Hotunan Buhari ya na tattakin mita 800, Obasanjo ya na kwallo, Jonathan ya na sassarfa

Wike yace Ukala ne ya jagoranci tsaya masa da baki ɗaya iyalansa har suka fita daga kalubale a wancan lokacin.

Gwamnan Ribas, Nyesom Wike
Yadda aka kama ni, mahaifina da yan uwana da zargin kisa, Gwamna Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Punch ta rahoto Gwamnan yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Akwai lokacin da baki ɗaya iyalaina aka zarge su da kisa. Baki ɗaya mazan aka kame mu, aka bar mata kaɗai da kananan yara dake shekara ɗaya zuwa biyar."
"A lokacin ina karantar Law a jami'ar kimiyya da fasaha ta jihar Ribas, wacce yanzu ake kira Jami'ar jihar Ribas."

Gwamnan ya kara da cewa babban lauyan, wanda ya yi aiki karkashinsa bayan kammala karatu, shi ne ya yi iyakar kokarinsa ya kubutar da su.

An zarge ni da fashi da makami - Wike

Wike yace lokacin da ya ayyana shirinsa na tsayawa takarar ciyaman a karamar hukumar Obio-Akpor a shekarar 1998, wasu yan siyasa a mazabarsa suka haɗa kai da yan sanda aka laƙaba masa sharrin fashi da makami.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: An nada Jose Peseiro matsayin sabon Kocin Super Eagles

A cewarsa, Ukala ba shiga lamarin kaɗai ya yi ba, sai da ya tsaya masa tun daga kotun hukunta masu laifi har zuwa kotun ƙoli yayin da wasu su kai kokarin tube shi daga ciyaman.

"Baki ɗaya lamarin ciyaman a shekarar 1998, har akai zabe a watan Afrilu 2000, har zuwa san da kotun koli ta yanke hukunci, Ukala bai taba ɗaukar naira ɗaya ba."

Bayan zaben gwamna a 2015

Wike yace lokacin da kotu ta soke zaben gwamnan Ribas a 2015, wanda ya samu nasara, ya tuntubi lauyoyi da dama domin tsaya masa a kotu.

Wasu sun nemi miliyan N300m zuwa N600m amma yana zuwa wurin Ukala, kyauta ya tsaya masa, inji shi.

A wani labarin kuma Malami ya bayyana yadda shugaba Buhari ya ceci Najeriya daga tarwatsewa a shekarar 2015 bayan zaɓe

Ministan yace Buhari ya samu ƙasar nan tana tangal-tangal, kuma ya ceto ta daga kifewar tattalin arziki, wanda ka iya watsa kasar.

Kara karanta wannan

Innalillahi: 'Yan bindiga sun kutsa gidaje a Zamfara, sun hallaka wani basarake

Malami yace shugaba Buhari ya yi abin da ba kasafai shugabanni ke iya yi ba cikin shekara ɗaya da hawansa karagar mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262