Da dumi-dumi: Shugaba Buhari ya amince da daukar ‘yan Najeriya 10,000 aikin ‘yan sanda

Da dumi-dumi: Shugaba Buhari ya amince da daukar ‘yan Najeriya 10,000 aikin ‘yan sanda

  • Hukumar 'yan sandan Najeriya ta kwashi 'yan Najeriya 10,000 aiki a matsayin jami'an 'yan sanda
  • Hakan ya biyo bayan samun yardar shugaban kasa Muhammadu Buhari, a kokarin da gwamnatinsa ke yi na magance matsalolin tsaro a wasu yankunan kasar
  • Hadimin shugaban kasa, Bahir Ahmad ne ya sanar da hakan a ranar Laraba, 29 ga watan Disamba

Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da daukar 'yan Najeriya 10,000 aiki a matsayin jami'an 'yan sanda.

Hakan na daga cikin kokarin gwamnatinsa na magance matsalolin tsaro da suka addabi yankuna daban-daban na kasar.

Da dumi-dumi: Shugaba Buhari ya amince da daukar ‘yan Najeriya 10,000 aikin ‘yan sanda
Da dumi-dumi: Shugaba Buhari ya amince da daukar ‘yan Najeriya 10,000 aikin ‘yan sanda Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

Kamar yadda mai ba shugaban kasa shawara kan kafofin sadarwar zamani, Bashir Ahmad ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce an dauki jami'an ne a fadin jihohi 36 na kasar da babbar birnin tarayya.

Kara karanta wannan

Tsohon shugaban kasar Gambia zai fuskanci fushin doka saboda kashe wasu 'yan Najeriya

Ya kuma bayyana cewa an zabi mutane goma-goma daga kowani kananan hukumomi 774 na kasar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Har wa yau, ya bayyana cewa tuni aka aikewa zababbun jami'an sako ta adireshin imel da suka yi rijista da shi.

Bashir ya wallafa:

"Kamar yadda Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da shi, hukumar 'yan sanda Najeriya (NPF) ta dauki 'yan Najeriya 10,000 aiki a matsayin jami'an 'yan sanda a fadin jihohi 36 na kasar da babbar birnin tarayya Abuja, domin magance matsalolin tsaro a wasu yankunan kasar.
"An zabi mutane goma daga kowani kananan hukumomi 774 na kasar, kuma tuni aka sanar da su ta adireshin imel da suka yi amfani da shi wajen neman aikin.
"An gode Baba!"

Buhari zai iya kawo karshen ta'addanci kafin cikar wa'adin mulkinsa, Femi Adesina

A gefe guda, Femi Adesina, mai magana da yawun shugaban kasa, ya ce yana sa ran za a ga bayan manyan 'yan ta'addan kasar nan kafin cikar wa'adin mulkin shugaban Buhari.

Kara karanta wannan

Buhari zai iya kawo karshen ta'addanci kafin cikar wa'adin mulkinsa, Femi Adesina

A yayin jawabi a wani shirin Channels TV, Adesina ya ce da irin kokarin da ake yi na inganta tsaro, za a iya ganin bayan rashin tsaro a cikin watanni 17 da suka rage na mulkin Buhari.

Adesina ya kara da cewa, shugaban kasa ya na aiki tukuru wurin ganin ya inganta rayuwar 'yan kasa, TheCable ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng