Kwarya tabi kwarya: Babu laifi don mutum ya dage sai daidai da shi zai aura, tsohon dan majalisar Kano

Kwarya tabi kwarya: Babu laifi don mutum ya dage sai daidai da shi zai aura, tsohon dan majalisar Kano

  • Abdulmumin Jibrin ya bayyana ra'ayinsa a kan batun kwarya tabi kwarya da ake yi a yankin arewa musamman a wajen aure
  • Tsohon dan majalisar na Kano ya bayyana cewa babu laifi don mutum ya ce lallai sai wanda suke a aji guda zai aura
  • Ya ce mutum na da yancin aure daga kowani mataki, imma daga babban gida ko kuma gidan marasa karfi

Tsohon dan majalisar dokokin Kano, Hon. Abdulmumin Jibrin, ya bayyana cewa ko kadan babu laifi don mutum ya dage kan auren wanda suke a aji guda a matsayin abokin rayuwa.

Jibrin, wanda ya wakilci mazabar Bebeji/Kiru na jihar Kano a majalisar wakilai, ya bayyana hakan ne a shafin Instagram a ranar Talata, 28 ga watan Disamba.

Kara karanta wannan

Bidiyon yadda wasu suka ba hammata iska a yayin da ake tsaka da wa’azi a coci

Hakan martani ne ga cece-kuce da ake yi kan dabi'ar mutanen arewacin Najeriya na son yin kwarya tabi kwarya musamman idan aka zo kan lamarin aure.

Kwarya tabi kwarya: Babu laifi don mutum ya dage sai daidai da shi zai aura, tsohon dan majalisar Kano
Kwarya tabi kwarya: Babu laifi don mutum ya dage sai daidai da shi zai aura, tsohon dan majalisar Kano Hoto: abdulabmj
Asali: Instagram

Sai dai kuma, ya bayyana cewa babu aibu don mutum ya aura daga dukkan matsayi... imma daga gidan talakawa ko babban gida.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Idan aka zo batun aure, ba laifi bane mace ko namiji ta auri aji - daga babba ko karamin gida (rashin adalci ne mutum ya tsaya a tsakanin irin wadannan aure idan har shine zabin abokan rayuwan. Amma babu laifi don mutum ya dage sai ya nemi abokin zama wanda suke a matsayi ko aji daya, Aure ibada ne ba nasara bane. Ka yi abun da zai fisshe ka amma kuma ka shirya ma abun da zai biyo baya! sannan idan ka tursasa ma wani irin abokin rayuwar da kake so, toh ka shirya ma abun da zai biyo baya."

Kara karanta wannan

Ba zata sabu ba: Iyayen amarya sun fasa aurar da 'yarsu bayan ganin gidan da ango zai aje ta

Ba ma son 'yar mu ta sha wahala: Iyayen amarya sun fasa aurawa ango 'yarsu bayan ganin gidan da za ta zauna

A gefe guda, wata budurwa ‘yar Najeriya mai suna Maryam Shetty a Facebook ta yada wani labari a shafinta, inda ta zayyana yadda aka fasa wani aure bayan samun karamar matsala.

Kafin ta ba da labarin, budurwar ta rubuta cewa al'adar nuna fifiko ya zama ruwan dare a yankin Arewacin kasar nan kuma iyaye ne ke aiwatar da shi.

Ta bayyana cewa kafin a soke auren, iyayen amaryar sun ji cewa gidan angon sam bai musu ba, kuma bai dace da matsayin ’yar su ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng