Rochas ya tona asiri: Babu 'yan bindiga a Imo, 'yan sanda ne daga gidan gwamnati ke kisa

Rochas ya tona asiri: Babu 'yan bindiga a Imo, 'yan sanda ne daga gidan gwamnati ke kisa

  • Kamun da aka yiwa Ugwumba Uche Nwosu a Nkwerre ta jihar Imo na ci gaba da haifar da ceceku daga 'yan siyasa
  • Owelle Rochas Anayo Okorocha ya ce lamarin ya nuna cewa Gwamna Hope Uzodimma ne ke haddasa rashin tsaro a Imo
  • Okorocha ya shaidawa wani gidan talabijin cewa wadanda ke tada rikici a Imo jami’an ‘yan sanda ne da ke aiki a gidan gwamnati

Jihar Imo - Sanata Rochas Okorocha a ranar Talata, 28 ga watan Disamba ya yi zargin wasu da aka bayyana a matsayin ‘yan bindiga da ba a san su ba da cewa ‘yan sanda ne daga gidan gwamnati da ke Owerri.

Okorocha, wanda tsohon gwamnan jihar Imo ne, ya yi wannan zargin ne a lokacin da yake zantawa da gidan talabijin na Channels a martanin da ya bayar game da kama Ugwumba Uche Nwosu.

Kara karanta wannan

"Yadda Gwamna mai-ci ya bada umarni a nemi ayi wa ‘Dan takarar Gwamna kusan zindir"

Sanata Rochas Okorocha, tsohon gwamnan Imo
Babu wasu 'yan bindiga, 'yan sanda ne daga gidan gwamnati ke kashe mutane, inji Okorocha | vanguardngr.com
Asali: UGC

Nwosu tsohon dan takarar gwamna a jihar, tsohon shugaban ma’aikatan Okorocha ne kuma surukin sa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jami’an ‘yan sanda dauke da bindigogi ne suka yi awon gaba da dan siyasar a wani coci a garinsu wanda ya janyo cece-kuce a fadin kasar.

Okorocha ya ce kama Nwosu a cikin cocin a ranar Lahadi, 26 ga watan Disamba, ya nuna yadda gwamnatin jihar Imo ke aikata miyagun laifuka tare da ‘yan sandanta dake gidan gwamnati.

A kalamansa, cewa yayi:

“Yan bindigan da ba a san ko su wanene ba yanzu ‘yan sanda ne daga gidan gwamnati, wadanda ba tare da izinin Kwamishinan ‘yan sanda, Sufeto Janar na ‘yan sanda, ko DIG ba, sai dai don radin kansu bisa umarnin gwamnatin jihar Imo, karkashin jagorancin Hope Uzodimma, da CSO, Shaba, wadanda ke ba da umarnin kama mutane yadda suke so da daure mutane yadda suka ga dama, wani lokacin kuma ba a sanin inda wadannan mutane suke."

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Yan sanda sun sako sirikin Sanata Okorocha da suka cafke

Martanin Deji Adeyanju kan kame Uche Nwosu a coci

A nasa bangaren, fitaccen dan gwagwarmaya, Deji Adeyanju ya mayar da martani game da kama Nwosu da karfi a cikin coci.

Adeyanju ya rubuta a shafinsa na Facebook cewa:

"Idan da an yi kuskuren kashe Uche Nwosu a lokacin da aka yi garkuwa da shi, da sun musanta kuma sun zargi kungiyar IPOB."

A wani labarin, Gwamna Hope Uzodimma ya sha alwashin bayyana sunayen wadanda ke da hannu wajen kai hare-hare a jihar Imo da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.

PM News ta ruwaito cewa gwamnan ya bayyana haka ne a wani taron masu ruwa da tsaki da za a gudanar a ranar Litinin 3 ga watan Janairu, 2022.

Ya yi bayanin cewa wasu mutane 18 ne da jami’an tsaro suka kama kwanan nan kan kashe kansiloli biyu a jihar, sun bayyana sunayen wadanda suke haddasa rashin tsaro, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta yi magana a kan cafke sirikin tsohon gwamna a wurin Ibada

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.