Ku sayi bindiga, ku kare kan ku: Masari ya yi kira ga al'ummar jiharsa

Ku sayi bindiga, ku kare kan ku: Masari ya yi kira ga al'ummar jiharsa

  • Gwamnan Masari na Katsina ja jaddada cewa jami'an tsaron Najeriya sun gaza kare al'ummarsa
  • A baya, Gwamnan ya dade yana fadin cewa adadin jami'an tsaron da Najeriya ke da su sun yi kadan
  • Yanzu Masari ya bayyana niyyar taimakawa duk wanda ke son mallakar bindgar kansa don kare kansa

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya yi kira ga al'ummar jiharsa su mallaki makamai don kare kansu daga hare-haren yan bindiga saboda jami'an tsaro kadai ba zasu iya ba.

Masari, wanda ya bayyana hakan yayin hira da manema labarai a Muhammadu Buhari House dake Katsina ya ce adadin jami'an tsaron da Najeriya ke da shi ya yi kadan wajen magance wannan matsala.

A cewarsa, ko addini ya amince da mutum ya kare kansa da dukiyarsa daga wanda ke kokarin kwacewa.

Kara karanta wannan

Gwamna a Najeriya ya bayyana yadda aka kama shi da mahaifinsa kan zargin kisa

A cewarsa:

"A addinin Musulunci ya halatta mutum ya kare kansa daga hari. Wajibi ne mutum ya kare kansa, iyalansa da dukiyarsa. Idan ka mutu kana kare kanka ka yi shahada."
"Da mamaki yadda za'a bari dan bindiga ya mallaki makami amma ace magidancin dake kokarin kare kansa bai mallaka ba."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ku sayi bindiga, ku kare kan ku: Masari ya yi kira ga al'ummar jiharsa
Ku sayi bindiga, ku kare kan ku: Masari ya yi kira ga al'ummar jiharsa Hoto: Press COnference
Asali: Twitter

Zamu taimakawa duk wanda ke son mallakar bindiga

Masari ya ce gwamnatin jihar za ta taimakawa duk wanda ke son mallakan makamai don kawo karshen matsalar tsaro.

Yace:

"Zamu taimakawa wanda ya zo da hanyar sayan makamai saboda jama'a na bukatan taimakawa jami'an tsaro."
"Wadannan jami'an tsaron ba su da yawan da zasu kare mutane. Ka kira da kanka, jami'an yan sanda nawa muke da su a kasar nan? Sojoji nawa muke da su?

Masari yace hukumar yan sanda za ta yi rijistan dukkan makaman da za'a siya don tabbatar da anyi abinda ya kamata da su.

Kara karanta wannan

Ayyukan yan binidga a Arewa: CAN ta maida martani ga gwamna Masari na jihar Katsina

Katsina: Za mu dage dokar dakile layikan sadarwa kafin watan Janairun, Masari

A wani labarin kuwa, Gwamnatin jihar Katsina ta ce za ta dage dokar datse layikan sadarwar da ta yi a kananun hukumomi 7 da lamarin ya shafa a watan Janairun 2022, Daily Trust ta ruwaito.

Gwamna Aminu Bello Masari na jihar ya shaida hakan yayin tattaunawa da manema labarai a ranar Talata a Katsina inda yace mazauna yankunan su kare kawunansu daga harin ‘yan bindiga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng