Dr Isa Pantami ya zub da hawaye kan yadda matasa sukayi wawaso a kantin da yayi gobara a Abuja
- Farfesa Isa Ali Pantami ya yi takaicin irin lalacewar matasa a wannan al'umma dake bukatan gyara da nasara
- Shehin Malamin kuma babban jami'in Gwamnati ya zub da hawaye kan yadda wasu matasa sukayi abin kunya
- A cewarsa, ta yaya wannan al'umma za tayi nasara idan matasanta zasu rika irin wannan hali
Abuja - Ministan Sadarwa da tattalin arzikin zamani, Farfesa Isa Ibrahim Ali Pantami, ya zub da hawayen takaici kan abinda wasu matasa suka yi a farkon makon nan a birnin tarayya Abuja.
A ranar Lahadi, 26 ga watan Disamba, mumunan gobara ya barke a kantin Next Cash and Carry dake unguwar Jahi, cikin garin Abuja.
Pantami ya yi takaicin lalacewar al'ummar matasa yadda maimakon taimakawa wajen kashe gobarar, wasu wawason kayan kantin sukeyi.
Ya yi wannan takaici ne a yayin karatun 'Birrul Walidayn' da ya saba gudanarwa mako-mako a Masallacin Annur dake2 unguwar Wuse II Abuja.
A bidiyon da Tribune ta daura a shafinsa na Facebook, an ga yadda Ministan ke takaici.
Malam Pantami yace:
"Da zu wani bala'i da na gani, gobara ake a Next Cash and Carry, mutane suna sata a wannan hali? Kaii (yana kuka)."
"Ta yaya zamu yi nasara a haka."
Kalli bidiyon:
Matasa sun shiga hannu yayin da suke kokarin satan kaya a wurin gobara a Abuja
Rundunar ‘yan sanda a babban birnin tarayya Abuja ta kama wasu mutane uku da suka yi yunkurin wawure wasu kayayyaki daga babban kanti na Next Cash and Carry da gobara ta kame a safiyar Lahadi.
Daily Trust ta ruwaito cewa, a cikin wani faifan bidiyo da ya yadu a yanar gizo, an ga matasa suna tura keken daukar kaya da ake zargin sun yi amfani da su wajen fitar da abubuwan suka sace
Sai dai da take karin haske kan halin da ake ciki a cikin wata sanarwa, rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja ta bakin mai magana da yawunta, Josephine Adeh, ta ce ba a sace kaya a kantin ba.
Asali: Legit.ng